Hukumar kula da sufurin Jirgin sama ta Nijeriya (NCAA) a ranar Litinin ta ce, zuwa yanzu an dakatar gwajin cutar Covid19 ga masu shigo wa ko fita cikin kasar nan, inda a yanzu bai zama dole sai an yi gwajin ba ga Fasinjojin da ke shigo wa ba.
A wata sanarwar da aka aike wa jami’an kula da sufurin Jirgin a fadin kasar nan dauke da sanya hannun darakta Janar na hukumar, Kaftin Musa Nuhu, ya ce, yanzu kuma sanya takunkumin rife fuska bai zama dole ga Fasinjojin jiragen sama a kasar nan ba.
- Kasar Sin Ta Inganta Matakan Yaki Da COVID-19 A Bangaren SufuriÂ
- Korona Ta Kusa Zama Tarihi A Duniya Baki Daya – WHO
A cewar Kaftin Musa bisa daukan matakan kariya na cutar da kasar Nijeriya ke yi, zuwa yanzu kasar ta samu nasara domin kuwa ba a samun karin yaduwar cutar tsawon lokaci.
Ya kara da cewa bai kuma zama tilas a sanya safar rufe baki da hanci a cikin filin jirgi ko cikin jirgi ko ga ma’aikatan filin Jirgin ba.
Ya ce, ga mai sha’awar sanya Takunkumin Fuska a bisa radin kashin kansa zai iya sanyawa amma ba wai dole ba ne yanzu.