Gwaman jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya koka kan cewa gwamnatin tarayya ba ta taimaka wajen kawo karshen rashin tsaro a wasu yankuna na kasar nan ba.
Matawalle ya kara da da cewa, gwamnatin ta gaza sauke nauyin da ke kanta na kare lafiya da kuma dukiyoyin ‘yan kasar nan.
- Gwamnatin Buhari Za Ta Yi Mai Yiwuwa Wajen Tabbatar Da Tsaro A Kasar Nan – Malami
- Jaridar Daily Trust Ba Ta Yi Mana Adalci Ba- Fadar Shugaban KasaÂ
A cewarsa jama’a da dama sun rasa rayukansu saboda ayyukan ‘yan bindiga a jihar Zamafara, inda ya kara da cewa hakan ne yasa gwamnatin ta fito daga tsarin bai wa Zamfarawa damar mallakar bindiga don su kare kansu daga hare-haren ‘yan bindigar.
Matawalle ya yi wannan koken ne a yayin da ya karbi bakuncin shugabanin kungiyar CSO a garin Maradu, inda ya ci gaba da cewa gwamtin na ba ta da wani karfin iko a kan Soji, ‘yan sanda da sauran Jami’an tsaro, inda hakan ya sa suka dauki matakin bai wa Zamafarawa damar mallakar bindiga bisa ka’ida domin su kare kansu.
A karshe, Matawalle ya sanar da cewa sun tattauna da ‘yan bindiga da ke addabar jihar Zamfara don a lalubu da mafita amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba, hakan ya sa suka kuma garkame kasuwanni da dakatar kafar sadarwa da hana sayar da man fetur a gidajen sayar da man jihar amma duk ba ta sake zani ba.