Gwamnatin Tarayya ta yi hadaka da kamfanin Google, domin kaddamar da shirin bayar da horo, bisa nufin tallafawa matasan kasar, masu yin sana’ar kirkira, guda 2,500.
Ta yi wannan hadakar ce, ta hanyar ma’aikatar kula da Al’adu da fannin kirkirar tattalin arziki.
- Sarki Sanusi II Zai NaÉ—a Babban ÆŠansa A Matsayin Ciroman Kano
- Super Eagles Ta Hauro Matsayi Na 36 A Jadawalin Duniya Na FIFA
Ana kuma sa ran a nan gaba, akalla wadanda za su amfana da shirin, za su kai yawan biliyan 10,000.
Cibiyar baya da horon kirkira ta Del York ce, za ta wanzar da shirin.
Hakazalika, shirin zai mayar da hankali ne, wajen bunkasa fasahar kirkira da kuma kara karfafa guiwar yin kirkira da kuma habaka yin da kamfanoni masu zaman kansu, da ke a fannin masana’antar kikira a kasar nan.
Shirin wanda ma’aiktar kula da al’adu tare cibiyar ma’aikatar al’adu ta kasa NCAC da kuma CLAP da za su wanzar da shi.
Babbar manufar shirin shi ne, don a karfafa guiwar matasa masu sha’awar fannin kirkira a kasar nan.
Ta hanyar yin hadaka da kamfanin na Google da Del York, wadanda za su amfana da horon, za a horas da su a bangarori kamar na wajen yin finafinai da sauransu.
Da take yin jawabi a kan mahiimancin hadakar ministan ma’aikatar kula da al’adu Hannatu Musa-Musawa, ta bayyana jin dadinta a kan wannan hadakar.
A cewarta, wannan hadakar, ta nuna yunkurin da ake da shi a kasar nan, na kara habaka zakakuran matasan da ke a fannin kir-kira a kasar.
Ta ce, samar da kayan aikin ga matasan da ke a fanin na kir-kira, ba wai kawai don a samar da ayyukan yi bane, har da ma kara daga darajar Nijeriya don ta zamo a kan gaba a duniya, a fannin wajen daga darajar al’adu.
Hannutu ta sanar da cewa, shirin na daya daga cikin kudurorin gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu da a turance, ake kira da Renewed Hope agenda, ta yadda za a tallafawa matasan da ke a fannin kir-kira, domin suma su bayar da ta su gudanmawar, wajen kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.
Haron na mako shida, zai samarwa wadanda za su amfana wani ginshiki kwarewa na yin kir-kira na sarrafa fina-finan bidiyo da sarrafa hotuna da sauransu.
Bugu da kari, daga cikn wadanda aka zabo, za a kuma bayar da wani horon na mako uku.
Olumide Falegan, manaja a sashen al’adu a kamfanin Google, ya jaddada mahimmanci da shirin yake da shi.
Ya ce, shirin zai taimaka wajen gano matasa da ke da kwarewa a masana’antar kirkira.
A cewarsa, baya ga tallafa kwarrun matasan su 2,500, ana kuma sa ran za’a kara fadada shirin zuwa ga matasa 10,000 da suma za su amfana a daukacin fadin kasar.
Shi kuwa babban shugaban rukunonin Del York Linus Idahosa, ya bayyana cewa, hadakar za ta ci ke gibin da ak da shin a samar da kwararu da masu ruwa da tsaki a fannin kir-kira.
An dai fara karbar takardun shiga shirin wadda aka bude a ranar 8 na watan Okutobar 2024, za kuma rufe karbar, a ranar 30n ga watan na Okutobar 2024.