Manyan jami’an gwamnatin tarayya da na jihohi sun baiwa al’ummomin da ke zaune a yankin manyan madatsun ruwa a arewacin Nijeriya tabbacin kubuta daga fargabar da ke tattare da su na ballewar madatsun.
Tun bayan afkuwar bala’in ballewar madatsar ruwa ta Alau a jihar Borno, al’umma sun shiga fargaba, inda suka yi zargin cewa, madatsun ruwa da ke sauran yankunan Arewa na cikin wani mummunan hali.
- Birtaniya Ta Bukaci ‘Yan Kasarta Su Gaggauta Ficewa Daga Lebanon
- Akwai Bukatar Shugabannin Arewa Su Farka – Sarkin Fawa
Ballewar madatsar ruwa da ta taba afkuwa a garin Goronyo da kewayen jihar Sokoto, ta sanya mazauna garin cikin damuwa bayan bala’in Borno, ganin cewa, hakan na iya afkuwa da su.
Saboda ire-iren wannan firgici, Ministan Albarkatun Ruwa, Engr Joseph Utsev ya kai ziyarar gani da ido wasu manya daga cikin madatsun ruwa da ke Arewacin Nijeriya, inda ya tabbatar da cewa, babu wata fargaba.
“Ana ta yada irin wannan jita-jita game da madatsar ruwa ta Dandin Kowa da ke Gombe amma da muka isa wurin sai aka gano cewa, jita-jita ce kuma karya ce.”
Dam din Dadin Kowa da ke jihar Gombe a kwanakin baya ya haifar da fargaba bayan da rahotanni suka bayyana cewa, zai iya ballewa sakamakon mamakon ruwan sama da ke zuba.
Daga cikin madatsun ruwan da aka bincika don gujewa irin bala’in da ya afku a Borno sun hada da:
Madatsun ruwa dake karamar hukumar Gusau, Bakalori dake karamar hukumar Maradun da Dangulbi dake karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.
A jihar Kano akwai Babbar Madatsar ruwa ta Tiga, Bagwai da Challawa.
Madatsar ruwa ta Asa da ke Ilorin a jihar Kwara, an tabbatar cewa, tana cikin kyakkyawar kula.
A jihar Neja, akwai manyan Madatsun ruwa guda hudu da suka hada da Kainji, Jebba, Shiroro da Zungeru.
Sai dai Ministan Albarkatun Ruwa, Engr Joseph Utsev ya tabbatar wa jama’a cewa, babu wani abin fargaba a duk madatsun ruwan.
A ziyarar da ministan ya kai a baya bayan nan, ya tabbatar da cewa, gwamnatin tarayya na daukar matakan kare madatsar ruwan.