Gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki domin mayar da shanun da suke yawo a cikin Abuja zuwa wuraren kiwo da aka tsara kuma aka tanadar.
Ministan bunƙasa harkokin kiwo, Dakta Idi Maiha, shi ne ya sanar da hakan a ranar Talata yayin taron ƴ an jarida na 2025, wanda ya gudana a Kaduna, inda aka maida hankali kan bunƙasa harkokin noma ta hanyar sadarwar da suka dace cikin dabaru na hikima.
“Abin da muka mayar da hankali a kai shi ne, a samu ƙasar da manyan motoci ɗauke da nono ba masu ɗaukar makamai ba. Ya kamata injinan nono su maye gurbin bindigogin,” inji shi.
Maiha ya ce fannin kiwo ya kasance babban jigon samar da tagomashin arziki, samar da ayyukan yi, samar da abinci, da kwanciyar hankali a karkara.
Ya ce ma’aikatar ta himmatu wajen samar da tsare-tsare da manufofin da suka kamata waɗanda su kai ga kyautata lamuran kiwo da inganta samar da nono a cikin ƙasar nan.
Da yake magana game da taron, Maiha ya ce sadarwa ita ce jigon ciyar da harkar kiwon dabbobi gaba, “Bayan wannan taron, muna sa ran za ku yi amfani da dabarun ku don ƙara faɗaɗa labarin fannin kiwo.
“Muna yaba wa ƴ an jarida bisa aikinku na ƙwarewa da muke sa ran za ku ci gaba da amfani da dabarun da suka dace wajen kyautata sashin kiwo.
“Rahotonin da kuke bayar sun taka rawar gani wajen tsara fahimtar jama’a game da manufofinmu da kuma yin tasiri kan manoma, makiyaya, masu zuba jari, da sauran masu ruwa da tsaki,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp