Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da Ba’amurken nan Mista Tigran Gambaryan ya yi kan wasu jami’an gwamnatin Nijeriya, tana mai bayyana shi a matsayin ƙarya da yaudara.
Gambaryan dai jami’in kamfanin Binance ne daga Amurka, wanda hukumar EFCC ta gurfanar a Nijeriya a 2024 bisa almundahanar kuɗi.
- Bayan Shekara 32 NPA Ta Samu Sahalewar Gwamnati Na Ƙara Haraji
- Sulalewar Likitoci Zuwa kasashen Waje: ‘Likita Guda Na Duba Masu Cutar Kansa 1,800
Kwanan nan ne Gambaryan ya fito ya ce wai Mashawarci na Musamman kan Tsaron Ƙasa, Malam Nuhu Ribadu, ya taɓa neman ya karɓi toshiyar baki ta miliyoyin kuɗi a hannun sa don kamfen ɗin siyasar sa, amma haƙar sa ba ta cimma ruwa ba.
Haka kuma ya ambaci cewa wasu ‘yan Majalisar Tarayya guda uku sun nemi ya ba su toshiyar baki ta dala miliyan hamsin ($50m).
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a wannan Juma’ar, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce gwamnati ta san da jita-jitar da Gambaryan yake yaɗawa, amma ba ta so ta mayar masa da martani duba da irin matsayar diflomasiyya da ta kai ga warware shari’ar sa.
Sai dai ya ce, dole ne a fayyace gaskiya don hana wannan yaudarar samun gindin zama.
Ya ce: “Karo na farko da Mista Gambaryan da tawagar sa suka zo Nijeriya, sun zo ne karan kansu ba tare da wata gayyata daga gwamnati ba. Sai dai da aka sanar da gwamnati wani batu na neman cin hanci a lokacin, sai aka buɗe bincike nan take, ko da yake babu wanda ya shigar da ƙorafi kai-tsaye.”
Ya bayyana cewa, ziyarar Gambaryan ta biyu ta kasance wani ɓangare na bincike kan yadda ake amfani da kamfanin hada-hadar kuɗi na Binance don sarrafa darajar naira.
Ya ce, amma binciken ya gamu da cikas sakamakon dabarun da Gambaryan da tawagar sa suka yi amfani da su.
Ministan ya ƙara da cewa, Gambaryan ya samu ‘yanci a watan Oktoba na 2024 bisa dalilai na jinƙai, bayan cimma matsaya tsakanin Nijeriya da Amurka da ta kawo fa’ida ga Nijeriya.
Ya kuma ce gwamnati ta yi watsi da tayin da Binance ya yi na biyan dala miliyan 5 domin a saki Gambaryan, inda ta amince da wata yarjejeniya mai amfani da gwamnatin Amurka.
“Muna ƙaryata duk wata magana da Mista Gambaryan ke yi kan jami’an gwamnati da ke da hannu a shari’ar sa, kuma muna kira ga jama’a da su yi watsi da waɗannan ƙarairayi baki ɗaya,” inji Idris.
Ministan ya bayyana cewa zargin da Gambaryan ke yi babu hujja, kuma bai da inganci duba da cewa yana ƙoƙarin ɓata suna da razana waɗanda suka tabbatar an gurfanar da shi a gaban shari’a ne.
Ministan ya ce yana da yaƙinin cewa, tsarin shari’a na Nijeriya da na Amurka za su ba Gambaryan damar gabatar da hujjoji kan zarge-zargen da yake yi.
A halin yanzu, ya buƙaci ‘yan ƙasa da su yi hankali kada su faɗa tarkon waɗannan ƙarairayi da ƙazafi da wannan Ba’amurken yake yaɗawa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp