Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya gargaɗi mutane kan ajiye abubuwa masu fashewa a gidajen su don haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, yana mai cewa irin wannan ɗabi’a tana haifar da babbar barazana ga rayuka da dukiyoyi.
Ministan ya yi wannan gargaɗi ne a ranar Laraba yayin da ya kai ziyarar jaje ga al’ummar Sabon Pegi a Jihar Neja, inda wata fashewar ɗanyen abu ta auku a ranar Litinin, ta haddasa asarar rayuka da lalata dukiyoyi.
- Gwamnati Ta Sake Haɗa Tubabbun Mayaƙan Boko Haram 5,000 Da Iyalansu
- Gwamna Mutfwang Ya Sallami Kwamishinoni Biyar
Tawagar ministan ta haɗa da Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago; da tsohon gwamna kuma Sanata mai wakiltar Mazaɓar Neja ta Arewa, Alhaji Abubakar Sani Bello; da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja, Alhaji Abdulmalik Sarkin-Daji, da wasu jami’an gwamnati.
Idris ya ce: “Waɗannan bala’o’i ne da yawancin su ɗan’adam ke haddasawa, kuma ba za mu bari su ci gaba da faruwa ba.
“Shugaban Ƙasa ya umarci Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) da ta ƙara ƙaimi wajen faɗakar da jama’a da wayar da kan ‘yan Nijeriya, musamman masu wannan haramtacciyar sana’a. Wannan yanki yana da albarkatun ma’adinai da dama.
“Kwanan nan, Ma’aikatar Raya Ma’adinai ta Tarayya ta fara gyaran tsarin haƙar ma’adinai a faɗin ƙasar nan, kuma muna fatan za su ɗauki wannan darasi da muhimmanci.”
Ministan ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni ga Ma’aikatar Raya Ma’adanai ta Tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen tsaftace harkar haƙar ma’adanai don kauce wa irin waɗannan haɗurran.
Haka kuma, ministan ya jaddada damuwar Shugaban Ƙasa kan yawaitar irin waɗannan bala’o’i a faɗin ƙasar nan, yana mai cewa dole ne a ƙara wayar da kan al’umma domin daƙile aukuwar irin su a nan gaba.
Ya ce: “Abu na farko da ya kamata mu gane shi ne irin wannan bala’i yana faruwa sau da yawa a ƙasar mu, kuma Shugaban Ƙasa yana cikin matsanancin baƙin ciki. Ya kuma umarta cewa Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa ta gudanar da wayar da kai da faɗakarwa, musamman a cikin waɗannan ƙauyuka, domin hana aukuwar irin hakan a nan gaba.”
A ƙarshe, Idris ya yaba da ƙoƙarin da gwamnatin Jihar Neja ta yi wajen ɗaukar matakin gaggawa game da lamarin, tare da bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta umarci Ma’aikatar Harkokin Jin Ƙai da Rage Talauci tare da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da su taimaka wa waɗanda abin ya shafa.