Gwamnatin tarayya ta amince da karin kasafin kudin da ya kai Naira tiriliyan 2.1.
Ministan Kasafin Kudi da tsare-tsaren Tattalin Arziki, Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa a ranar Litinin bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a fadar shugaban kasa.
- Shirin Blue Circle Na Kasar Sin Ya Samu Lambar Yabo Ta Kare Muhalli Daga MDD
- Ku Bayar Da Yaranku A Yi Musu Allurar Ragafin HPV Domin Ba Ta Illa Ko Kadan -Mansura Isa
Bagudu ya bayyana cewa, “Mun gabatar da wani karin kasafin kudi inda majalisar ta amince da karin Naira tiriliyan 2 da biliyan 176 da miliyan 791, da dubu 286 cikin kasafin kudin da aka gabatar.”
A cewarsa, karin kasafin kudin an yi shi ne don magance matsalolin da suka kunno kai, ciki har da ware biliyan 605 don harkokin tsaro domin ci gaba da samun nasarar da aka samu a baya.
Bagudu ya ce, an ware biliyan 300 domin gyaran gadoji, gine-gine sannan kuma an ware biliyan 200 don harkokin noma.
Ya kara da cewa, an samar da karin biliyan 210 don biyan karin albashi da gwamnatin ta cimma matsaya kan tattaunawarta da kungiyoyin kwadago, wanda za a fara biya daga watan Satumba zuwa Disamba 2023.
Bagudu ya bayyana cewa, an ware biliyan 400 domin biyan kudaden musayar kudi, inda ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta samu dala biliyan 800 daga bankin duniya na tsawon watanni biyu, kamar yadda shugaban kasa ya amince da a sanya a cikin kasafin kudin.
Ministan ya bayyana cewa, an amince da kudi har biliyan 100 don tallafawa babban birnin tarayya Abuja, domin gudanar da ayyuka na gaggawa yayin da aka ware biliyan 18 ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) domin gudanar da zabe a Bayelsa da kuma Jihar Imo.
Ya ce, an ware karin biliyan 5.5 domin gudanar da ayyukan kaddamar da rancen kudi ga dalibai, kuma an ware biliyan 800 domin shirye-shiryen kafa sabuwar ma’aikata.
Yarjejeniyar da aka cimma da kungiyoyin kwadago na karin albashi har na tsawon watanni shida na nan daram bata canja ba.