Gwamnatin Tarayya ta bayyana Talata, 15 ga Yuli, 2025, a matsayin hutu na musamman don girmama tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu ranar Lahadi, 13 ga Yuli, yana da shekara 82.
Ministan Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da sakatariyar dindindin ta ma’aikatar, Dr. Magdalene Ajani, ta fitar. Wannan hutu ya biyo bayan makon jimamin ƙasa guda ɗaya da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana domin tunawa da marigayin.
- Ina Cike Da Alhinin Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari — Atiku
- An Tsaurara Matakan Tsaro A Daura Gabanin Jana’izar Buhari A Gobe Talata
Sanarwar ta bayyana cewa hutun na Talata wata alama ce ta girmamawa ga irin gudummawar da marigayin ya bayar wajen ci gaban ƙasa, a matsayinsa na shugaban Soja daga 1983 zuwa 1985, da kuma shugaban da aka zaɓa a 2015 zuwa 2023. Gwamnatin ta yi kira da a yi amfani da ranar wajen yin tunani kan rayuwarsa da irin ɗabi’un da ya tsaya kai da fata a kansu.
Har ila yau, gwamnati ta buƙaci ƴan ƙasa su ci gaba da raya manufofin zaman lafiya da kishin ƙasa da haɗin kai da marigayi Buhari ya yi fama da su a rayuwarsa ta siyasa. An kuma umurci a ci gaba da sassauta tuta har zuwa Asabar, 19 ga Yuli, 2025.
A ƙarshe, gwamnatin tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayin, al’ummar Jihar Katsina, da dukkan ‘yan Nijeriya, tana addu’ar Allah Ya jikan marigayin da rahama kuma Ya ba ƙasa da ƴan ƙasa ƙarfin jure wannan babban rashi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp