Gwamnatin tarayya ta sanar da janye shirinta na siyar da tallafin buhunan shinkafa mai nauyin kilo 50 ga ma’aikatan gwamnati kan Naira 40,000.
An sanar da matakin ne ta wata takardar sanarwa mai taken, “Janye shirin siyar da tallafin shinkafa ga Ma’aikatan Gwamnati,” wanda babban sakataren ma’aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnati bangaren jin dadin ma’aikata ya sanyawa hannu.
- Jihar Katsina Ta Kafa Kwamitin Rabon Shinkafar Da Tinubu Ya Bayar
- Jami’an Tsaro Sun Yi Wa Ofishin NLC Dirar Mikiya Don Neman Hujja Kan Zanga-zangar Yunwa
Sanarwar wacce aka aike wa Daraktoci da Shugabannin Ma’aikatun, ta bayyana cewa, “An umurce ni da in tsinkayar da ku kan sanarwar da Ma’aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnatocin tarayya ta fitar ta ranar 1 ga watan Agusta, 2024 kan batun siyar da buhunan shinkafa na tallafi ga ma’aikata, yanzu an janye batun”
Babu wani dalili da ya sa aka dakatar da shirin ba zato ba tsammani, lamarin da ya jefa ma’aikatan gwamnati da dama da suka yi rajistar tallafin shinkafar cikin rudani.
Ministan yada labarai, Idris Mohammed ne ya sanar da shirin tallafin tun farko a Abuja inda ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta kudiri aniyar rage radadin matsalar karancin abinci da ake fama da ita ta hanyar siyar da buhunan shinkafa masu nauyin kilo 50 akan Naira 40,000 ga ma’aikatan gwamnati.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, wata takarda da ta gabata daga ma’aikatar mai kwanan wata 1 ga watan Agusta mai dauke da sa hannun daraktar kula da jin dadin ma’aikata, Misis Jaiyesim Abimbola Aderonke, ta bayyana tsarin yadda ma’aikatan gwamnati za su bi wajen sayen shinkafar.
Talla