Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), sun fara tattaunawa a Abuja domin dakile shirin yajin aikin da kungiyar ke kokarin tsunduma.
Ana gudanar da taron ne dai bayan da kungiyar ASUU ta yi barazanar shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani saboda gazawar gwamnati na kin aiwatar da yarjejeniyoyin da kungiyar ta kulla da ita a baya.
- Wang Yi Da Jake Sullivan Sun Tattauna Kan Sabon Zagayen Tattaunawa Tsakanin Shugabannin Kasashen Biyu A Nan Gaba
- FOCAC Ba Wani Dandali Na Tattaunawa Kawai Ba Ne
Taron wanda ke gudana a dakin taro na ma’aikatar ilimi ta tarayya, ana kallon taron a matsayin wani muhimmin kokari na hana tabarbarewar harkokin ilimi a jami’o’in gwamnatin Nijeriya.
Tun a ranar Litinin da ta gabata ne aka shirya tattaunawar amma an dage tattaunawar ba tare da wani bayani ba.
To sai dai kuma a wani taron karawa juna sani na cika shekara guda a kan karagar mulki, Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya tabbatar da cewa za a tattauna da ASUU nan ba da jimawa ba.
Shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya wakilci ASUU a taron, tare da tsoffin shugabannin kungiyar, ciki har da tsohon shugaban kungiyar, Farfesa Biodun Ogunyemi.