Gwamnatin tarayya ta bayyana alhininta dangane da fashewar wata tankar man fetur a garin Essa da ke karamar hukumar Katcha a jihar Neja, wacce ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da dama.
A wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Laraba a Abuja, Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ya bayyana lamarin a matsayin “abin takaici” tare da mika ta’aziyya ga gwamnati ga iyalan wadanda abin ya shafa da kuma al’ummar jihar Neja.
- Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.5 Na Aikin Haƙo Uranium, Mai Da Iskar Gas
- ‘Yansanda Sun Cafke Wani Matashi Ɗan Shekara 15 Da Ake Zargi Da Yin Fashi Da Makami A Gombe
Sanarwar ta kara da cewa, “Muna tare da gwamnati da al’ummar jihar Neja wajen alhinin wannan babban rashi.” “Wannan lamari mai kaɗa zuciya ya sake haifar da mummunar illar hadurran tankar mai a cikin al’ummominmu.”
Gwamnatin Tarayya ta koka da cewa, duk da wayar da kan jama’a da kuma gargadin da ake ci gaba da yi, wasu mutane har yanzu suna kasada da rayukansu ta hanyar yunƙurin ɗibar mai yayin da tankunan dakon mai suka faɗi.
Ya jaddada cewa, kowace rai ta ɗan Nijeriya tana da daraja kuma irin wadannan bala’o’in da za a iya rigakafin su, na nuna bukatar kara wayar da kan jama’a game da haɗurran da ke tattare da hakan cikin gaggawa.
Ya ce, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), an umurce ta da ta hada karfi ga kokarin Gwamnatin Jihar ta hanyar samar da kayan agaji da taimakon magunguna ga wadanda abin ya shafa da iyalansu.