Gwamnatin Tarayya ta kafa wani kwamiti da zai yi nazarin halin da dukkanin madatsun ruwan Nijeriya ke ciki bayan ambaliyar ruwan da ta auku a Jihar Borno.
Wannan dai na daga cikin kudurorin da aka cimma a taron majalisar zartarwa da Shugaban Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin.
- Tsohuwa Ta Yi Barazanar Kai Ƙarar Wanda Ya Shirya Gasar Cin Taliya Da Jikanta Ya Lashe
- Ba Kare Bin Damo Tsakanin Man City Da Arsenal A Etihad
Ministan yada labarai, Mohammed Idris ne, ya shaida wa manema labarai cewar, a kowane lokaci idan abu ya faru mara dadi ko kuma wanda za a dauki darasi a kansa, to gwamnati kan sake lamarin don kaucewa faruwar hakan a gaba.
Ya ce, “Ba daidai ba ne idan an samu makamancin abin da ya faru a Maiduguri a yi shiru kamar babu abin da ya faru, hakan ne ya sa majalisar zartaswa ta yi tunanin cewa ba kawai maganar madatsar ruwa ta Alau ba, akwai bukatar a sake duba duk wata madatsar ruwa da ke Nijeriya.
“Kwamitin da aka kafa yanzu zai sake duba dukkanin madatsun ruwa don tabbatar da cewa ba a sake samun aukuwar irin abin da ya faru a Maiduguri ba.”
Idris, ya ce a yanzu gwamnati ta yi duk abin da ya kamata dangane da batun cikakken bayani a kan wannan kwamiti.
Ambaliyar dai ita ce mafi muni a Jihar Borno cikin shekaru 30, saboda ta shafe sassan Maiduguri da dama.
Lamarin dai ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi marasa adadi a jihar.