Ana sa ran fannin aikin noma na zamani, zai kara habaka a Nijeriya, biyo bayan isowar Taraktocin noma 2,000 rukunin farko daga Kasar Belarus.
Idan za a iya tunawa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tuni ya amince da sayo Taraktocin noman 2, 000 daga Kasar Belarus.
- Ba Gwamna Bala Ne Ya Soke Hawan Daushe Ba – Masarautar Bauchi Ta Bayyana Gaskiya
- Fashin Baki Kan Kasafin Kudin 2025 Na Naira Tiriliyan 54.99
Ministan Aikin Gona da Samar da Wadacacen Abinci, Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka.
Kyari ya sanar da hakan ne, a yayin da ya kai ziyarar gani da ido ta bazata, domin ganin Taraktocin noman guda 2, 000 da suka fara isowa cikin kasar.
“Mun ji dadi da fara karbar wannan rukuni na farko na wadannan Taraktocin noman 2, 000, wanda hakan ya nuna cewa; mun karbi kasshi 30 cikin 100 na kayan”, a cewar Kyari.
“Wadannan Taraktocin noma 2, 000, za a tura su don fara yin noman daminar 2025 da su, wadanda kuma za a iya horas da matasa a kananan hukumomin kasar 774, har ila yau, muna da wadatattun kayan gyaransu da za a iya yin aikin da su har tsawon shekara hudu”, in ji shi.
A yayin da Kyarin ya kai ziyarar aiki domin duba Taraktocin, ya nuna jin dadinsa kan ci gaban da ake samu na hadakar da gwamnatin tarayya ta yi da kasar ta Belarus, musamman domin samar da kayan aikin noma na zamani.
Kasashen biyu, sun kulla wannan yajejeniyar ce a watan Satumbar 2024.
“A yanzu da nake magana da ku, sama da kwantena 200 da suka yi dakon Tarakatocin da kayan gyaransu, sun iso Jihar Legas, inda ya kara da cewa, a karkashin wannan shiri; an turo Taraktoci 2,000 wadanda kowacce daya ke dauke da kayan gyaranta 9,072”, in ji Kyari.
Ministan ya kara da cewa, samar da wadannan Taraktoc, na daya daga cikin alkawuran yakin neman zabe da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi, musamman duba da cewa; gwamnatin ta mayar da hankali wajen farfado da fannin aikin noma na wannan kasa.
Tsarin Rabar Da Taraktocin:
Gwamnatin tarayya, ta shirya tsari uku na rabar da wadannan kayayyaki, wadanda suka hada da; sayarwa kai tsaye ga daidaikun mutane, sayar wa da kungiyoyi da wadanda za su karbi haya.
Ana sa ran Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne, zai kaddamar da wadannan Taraktoci kafin a fara noman kakar bana da su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp