Gwamnatin tarayya ta kare shirin ci bashin da ta ke yi, tana mai cewa an yi hakan ne bisa amincewar majalisar tarayya, duk da cewa hukumomin samar da kuɗaɗen shiga sun samu abinda suke hasashen samu na shekara.
Wannan bayani ya fito ne a taron tattaunawa tsakanin hukumomin samar da kuɗaɗen shiga da kwamitocin haɗin gwuiwa na majalisar tarayya kan kuɗi, da kasafin kuɗi, da tsare-tsaren tattalin arziki a Abuja.
- Nijeriya Na Iya Samun Naira Tiriliyan 6.9 Na Kudin Shiga Daga Mai A Wata Daya
- Gwamna Biodun Ya Amince Da ₦70,000 Mafi Ƙarancin Albashi Ga Ma’aikatan Ekiti
A taron, hukumar Kwastam ta bayyana cewa ta tara Naira tiriliyan 5.352 har zuwa Satumba 2024, wuce Naira tiriliyan 5.09 na shekara da suke don samu. Haka kuma, NNPCL ta ce ta tara Naira tiriliyan 13.1, wuce kuɗin da suke burin samu na Naira tiriliyan 12.3 na 2024, yayin da FIRS ta bayyana cewa ta tara kuɗaɗen harajin da suke burin samu har da Naira tiriliyan 5.7 daga kamfanoni.
Duk da ƙaruwar kuɗaɗen shiga, ‘yan majalisa sun tambayi dalilin da yasa gwamnati ke ci gaba da neman rance a wajen Nijeriya?
Ministan kasafin kuɗi, Atiku Bagudu, ya bayyana cewa shirin cin bashi yana cikin kasafin kuɗin 2024 da aka tsara don magance gibin Naira tiriliyan 9.7. Ya ce, duk da ƙaruwar kuɗaɗen shiga, akwai buƙatar bashi domin cike gibin kasafi da tallafawa talakawa da marasa galihu.
Duk da haka, hukumar kula da shige da fice ta fuskanci suka kan yarjejeniyar PPP da ta bai wa kamfani 70% na kuɗin fasfo, inda aka umarce su da miƙa dukkan takardun yarjejeniyar domin duba wa nan da mako guda.