Hukumar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kayayyaki ta Gwamnatin Tarayya ta maka kamfanin MultiChoice Nigeria, mamallakin DSTV da GOtv, a kotu bisa zargin karya dokoki.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, hukumar Federal Competition and Consumer Protection Commission (FCCPC), ta bayyana cewa ta ɗauki wannan mataki ne sakamakon ƙin bin umarnin da ta bai wa kamfanin.
- Gwamna Lawal Ya Yaba Da Yadda Aikin Filin Jirgin Saman Zamfara Ke Tafiya
- Kasar Sin A Matsayin Katafariyar Cibiyar Kere-Keren Mutum-Mutumi A Duniya
A ranar 24 ga watan Fabrairu, MultiChoice ya sanar da ƙarin kuɗin da ake biya don kallon DSTV da GOtv, wanda aka fara aiwatarwa daga ranar 1 ga watan Maris.
Wannan ƙarin kuɗin ya jawo suka daga ‘yan Nijeriya, lamarin da ya sa hukumar FCCPC ta buƙaci kamfanin da ya dakatar da ƙarin har sai an kammala bincike.
Sai dai hukumar ta ce MultiChoice bai bi umarnin ba, har ma ya ci gaba da aiwatar da sabon tsarin kuɗin da ya sanar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp