Shugaban Hukumar Sadarwar Nijeriya NCC, Dakta Aminu Maida, ya bukaci kamfanin waya ta Nokia ya kara zuba jari a bangaren bunkasa kimiyyar sadarwa a Nijeriya (ICT).
Dakta Maida ya yi wannan bayanin ne a lokacin da tawagar shugabannin gudanarwa kamfanin ‘Nokia Networks’ daga kasa Finland a karkashin jagorancin karamin ministan kasashen wajen kasar, Jarno Syrjala, suka kai masa ziyara don fadada hanyoyin karfafa mu’amala a tsakanin kasashen biyu.
- Har Yanzu Ƙanjamau Na Kashe Mutum Guda Duk Bayan Minti Ɗaya – Majalisar Ɗinkin Duniya
- Har Yanzu Ƙanjamau Na Kashe Mutum Guda Duk Bayan Minti Ɗaya – Majalisar Ɗinkin Duniya
Ya bayyana wa tawagar cewa, Nijeriya a shirye take wajen amfana da kwarewar Nokia wajen tallafa wa matasanmu samun masaniya a bangaren fasahar sadarwa.
Gwamnatin Nijeriya na shirin horas da matasa miliyan 3 a bangaren kimiyyar sadarwa, a kan haka muke fatan Nokia za ta jagoranci ba mu goyon baya don cimma wanann manufar, in ji shi.