Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shattima ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta tallafa wa masu ƙananan sana’o’i da naira biliyan 75, domin bunƙasa ƙananan da matsaƙaitan sana’o’i a faɗin Nijeriya.
Mataimakin shugaban ƙasa ya bayyana haka ne a wajen taron bunƙasa ƙanana da matsaƙaitan sana’o’i karo na 9 da aka gudanar a Jihar Katsina.
A cewarsa, ba da wannan tallafi na daga cikin ƙoƙarin da gwamnatin Tinubu take yi na hanyan samar da yanayin tattalin arziki ƙasa mai ƙarfin gaske.
- Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Masu Ƙananan Sana’o’i Biliyan 75 Domin Bunƙasa Kasuwancinsu
- EFCC Ta Ƙwato Kadarorin Naira Biliyan 500 A Ƙarƙashin Gwamnatin Tinubu – Shettima
Sanata Kashim ya bayyana wannan tallafi na naira miliyan 75 da gwamnatin Tinubu ta bayar a matsayin wakilci na irin ƙoƙarin da shugaban ƙasa ke yi na farfaɗo da tattalin arziki daga magagin da ya tsinci kansa a ciki.
Ya ƙara da cewa duk wani mai ƙoƙari da tsayuwa kan kasuwanci to, ya cancanci samun wannan tallafi domin ta haka ne tattalin arziki zai bunƙƙasa cikin sauri da samun sakamako mai kyau.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa kwamitin shugaban ƙasa kan ba da tallafi ya ƙaddamar da rabon naira miliyan 50, inda mutum miliyan 1 za su samu naira dubu hamsin kowanensu tare da wasu shirye-shirye na bunƙasa ƙananan sana’o’i.
Ya ƙara da cewa ƙanana da matsaƙaitan sana’o’i a Jihar Katsina za su samu 250,000 daga gwamnatin tarayya wanda zai taimaka wa sana’o’insu wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatinsa tana aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya wajen ƙirƙirar ayyuka, wanda yanzu haka an samar da kuɗaɗai har naira biliyan 5.5, inda aka raba biliyan ɗaya ga mutane 701 a faɗin jihar.
Gwamna Raɗɗa wanda ya ce gwamnati da ta kafa cibiyoyi da dama a Jihar Katsina domin kula da kayan sawa da sarrafa abinci da sauran su, kuma gwamnati a shirye take domin farfaɗo da masana’antu.













