Gwamantin tarayya ta samu naira tiriliyan 1 da digo 188 (N1.188t) daga kudaden haraji na (VAT) cikin wata shida na shekarar 2022.
Bayanai daga hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta nuna cewa an samu karin kaso 18.14 cikin dari idan aka kwatanta da kudin haraji na tiriliyan N1.0t da aka samu a farkon shekarar 2021.
- Majalisar Dattawa Na Neman A Kara Harajin Ilimin Manyan Makarantu
- Kotu Ta Yankewa Eto’o Hukuncin Watanni 22 Saboda Kin Biyan Haraji
Bayanan ya nuna cewa Nijeriya ta samu VAT na biliyan N600.15 a zango na biyu na 2022.
Wanda ke nuni da cewa an samu karin kaso 1.96 cikin dari daga biliyan N588.59 da aka samu daga farkon zangon 2022.
NBS ta ce harajin da aka samu na cikin gida ya kai biliyan N359.12 na zango na biyu na 2022.
Sannan kuma Nijeriya ta samu biliyan N111.13 na kudaden harajin da aka biya na waje a zango na biyu na 2022.