Gwamnatin Tarayya ta sanar da sauya sunan Jami’ar Abuja (UniAbuja) zuwa Jami’ar Yakubu Gowon.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnati a ranar Litinin bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya da shugaban kasa Bola Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin.
- Minista Ya Buƙaci Jihohi Su Sake Tunani Kan Duk Wani Yunƙurin Rushe Ma’aikatun Yaɗa Labarai
- Ƙaramin Ministan Mai Ya Yaba Wa Tinubu Kan Samar Da Cibiyar Lantarki A Maiduguri
An canza sunan ne domin karrama tsohon shugaban kasar Nijeriya, Janar Yakubu Gowon (rtd), wanda kwanan nan ya cika shekaru 90 a duniya.
Idris ya bayyana cewa, za a mika wannan kudiri ga majalisar dokokin kasar domin amincewa da shi a hukumance.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp