Hukumar lafiya ta duniya ta kiyasta cewar ana iya maganin kansar mahaifa idan har aka samun yi ma kashi 90 na ‘yan mata allurar rigakafi ta kwayar cuta mai suna Human Papillo Birus.
Gwamanatin tarayya ta kammala shirye- shiryen da suka kamata domin gabatar da allurar da zata ceci rayuwar mata matasa wajen yi masu allurar rigakafin kansar mahaifa allurar rigakafi mai suna Human Papillomabirus (HPB) wadda zata kare ‘yan mata daga kamuwa da cutar kansar mahaifa da sauaran cututtuka masu ala ka da ita.
Darektan hukumar kula da lafiya matakin farko Dakta Faisal Shuaib, shi ya bayyana hakan ranar Litinin a Abuja lokacin da aka yi taro da Shugabannin addini kan halin da hukumar take ciki.
Mista Shuaib ya ce gwamnatin zata fara yin allurar ne ranar 25 ga watan Satumba ga ‘yan mata masu shekara 9 zuwa 15.
Ya ce kansar mahaifa tana shafar iyayenmu,’yan’uwanmu, ‘ya’yanmu mata da suke kamuwa da cutar ta hanyar kwara HPB”.
“Ranar 25 ga watan Satumba wannan shekara za mu fara yi ma ‘ya’yanmu mata masu shekara 9 zuwa 15 allurar rigakafin kamuwa da kansar mahaifa.”
Kwayar Cutar HPB Da Kansar Mahaifa
Kansar mahaifa wata nau’in cutar kansa ce da take girma cikin mahaifar mace, ita ceta hudu da aka fi sani a tsakanin mata a duniya.Masana sun ce a shekarar 2008 kadau cutar kansar mahaifa ta yi sanadiyar mutuwar kamar yadda aka kiyasta mutuwar mata 311,000 a fadin duniya.
Binciken da Lancet suka yi ya nuna cewar fiye da mata milyan 44 na iya kamuwa da cutar kansar mahaifa tsakanin shekarar 2020 da 2069.
Hakanan ma ta yi gargadin cewa ana iya samun karuwara mutuwa daga kansar mahaifa ada abin zai iya kaiwa kashi 50 nan da shekara ta 2040, bugu dakari mata da yawa al’amarin zai shafar iyalansu da al’umma.
Duk da yake ba a san abinda yake sa ana kamuwa da cutar kansar mahaifa ba sai dai 14 daga cikin 100 na kwayar cutar mai suna Human Papillomabirus (HPB) an gano cewa sune musabbabin kamuwa da a kalla kashi 99 na wadanda suka kamu da cutar kansa.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce nau’oin kwayar cuta ta,HPB 16 da 18 sune musabbabin a kalla kashi 70 na nau’oin kansar da kuma kafin kamuwa da ita cutar.
Akwai ma sheda da ta hada kwayar cuta HPB da nau’oin kansa na dubura,wani sashe na farji, farji, azzakari, da oropharynd.
“Allural rigakafin kwayar cutar HPB tace wani cigaban daya shafi al’amarin kula da lafiyar al’umma.Wani abu ne mai nuna hadin kanmu wajen kare mutuncin rayuwa kjamar yadda Shu’aib ya jaddada”.
Gidunmawar Shugabannin Addini
Mista Shuaib ya ce yana da yana da kyau a samiu wayar da kan al’umma ko ina suke hakan ta sa gudunmawar Shugabannin ta taso.
Sune ke da damar sadar da sako mai muhimmanci wanda zai yi tasiri kan al’umma da kawar da shakku, su bada kwarin gwiwa na amincewa da sakon da ake son isarwa zuwa gare su,su yarda da tsarin da zamani ya zo da shi ta hanyar gwamnati.
“Ya ce kalamansu suna da matukar tasiri ga al’umma su amince har ga zuciyar su saboda mutuntawa da girmamawar da suke yi masu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp