Shugaban kasa Bola Tinubu, a ranar juma’a ya kori shugaban hukumar kimiyya da kere-kere ta kasa (NASENI), Dakta Bashir Gwandu.
Kazalika, Tinubu ya kuma amnce da nadin Khalil Suleiman Halilu mai shekaru 32, a matsayin wanda zai cike gurbin Dakta Gwandu.
Bisa nadin na Khalil Suleiman Halilu, zai shafe shekaru biyar akan karagar shugabancin hukumar wanda ya yi daidai da sashen dokar hukumar ta shekara 2014.
Korar ta Gwandu na kunshe ne a cikin sanawar da mai magana da yawun fadar shugaban kasa Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Juma’a.
Kazalika, sanawar ta ce, ana sa ran sabon shugaban hukumar Khalil zai yi amfani da kwarewarsa wajen bunkasa kimiyyar kasar nan.