Gwamnatin tarayya ta hannun babban sakataren Hukumar Baiwa Dalibai Bashi, Dr. Akintude Sawyer ya sanar da shirinta na kaddamara da baiwa daliban manyan makarantu Bashi.
Wannan na zuwa ne yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa kan lamarin, wanda ya ce, an kirkiro shirin ne don magance irin matsalar da dalibai ke fuskanta musamman ta fannin kudi.
- Masu Sana’ar Bola-jari Sun Buƙaci Gwamnatin Nijeriya Ta Tallafa Musu Da Rancen Kuɗaɗe
- Wani Jariri Ya Ɓata A Asibitin Waziri Gidado Da Ke Kano
Sawyer yace, bashin ba shi da ruwa, wanda hakan zai bawa daliban damar biya cikin kankanin lokaci, sannan kuma a samu damar bawa wasu daliban.
Babban sakataren yace, za’a kaddamar da shirin ne ta hanyar da dalibai zasu samu sauki, wajen cikewa tare da samun bashin cikin sauki, inda yace, za a yi amfani da manhaja ne ta yadda daliban za su cike bayanansu cikin sauki.