Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa tana shirin kara yawan harajin da ta ke karba.Â
Ministan KuÉ—i, Wale Edun ne, ya bayyana hakan yayin wani taron masu zuba jari a lokacin taron shekara-shekara na Bankin Duniya da ake gudanarwa a birnin Washington DC na kasar Amurka.
- Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Matsalar Lalacewar Wutar Lantarki A Nijeriya
- Tsarin BRICS Na Samun Karin Karbuwar Kasashe Daban-Daban
A cewarsa karin zai fi shafar kayan alatu ne.
Edun, ya jaddada cewa, karin harajin na hannun Majalisar Ƙasa domin ta duba tare da yin nazari.
Ya tabbatar da cewa kayan bukatun yau da kullum da talakawa da marasa galihu ke amfani da su ba za su shiga cikin karin ba.
Edun ya bayyana cewa za a fitar da jerin kayan bukatun yau da kullum da harajin ba zai shafe su ba.
Ya nuna cewa Shugaba Bola Tinubu ya kuduri aniyar kare talakawa yayin da ake aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da suka zama dole.
A watan Satumba, Shugaban Kwamitin Manufofin Kudi da Gyara Haraji na kasa, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa sun gabatar da shawarar kara harajin VAT daga kashi 7.5 zuwa kashi 10 a shekarar 2025.
Ya jaddada cewa tsarin kudin shigar Nijeriya yana cikin mawuyacin hali, kuma karin yana cikin matakan magance matsalolin kudin kasar.