Nan bada dadewa ba gwamnatin tarayya za ta fara raba tallafi na musamman ga masu kananan masana’antu wannan na daga cikin shirin gwamnatin Bola Tinubu na rage musu radadin matsin da janye tallafin man fetur ya jawo.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin Ministar masana’atu da kasuwanci, Dakta Doris Uzoka-Anite, ta kuma kara da cewa, shirin ya kunshi tsarin tallafi kashi biyu, za kuma a raba wa kananan masana’antun da suka cika dukkan ka’idojin da aka gindaya.
- CBN Zai Haramta Harkokin Kudi A Asusun Bankin Da Babu BVN Da NIN A 2024
- Tattalin Arzikin Nijeriya Zai Farfado Nan Da Wata 15 – Shettima
Sanarwar ta kuma kara da cewa, a cikin kashi na farko za a raba wa kananan masana’antu N50,000 a kananan hukumomi 774 da ke fadin tarayyar kasa nan.
“Gwamnatin tarayya za ta hada hannu da ma’aikatan masana’antu da kasuwanci da hukumnar kula da kananan masana’antu za kuma a nemi hadin kan gwamnati jihohi da kananan hukumomi da kuma ‘yan majalisun tarayya da bankuna da kuma dukkan masu ruwa da tsaki don ganin an samu nasarar rarraba kudaden.
“Kananann masana’antun da suka cancanta za su samar da takardun shaidan da suka kamata wadanda suka hada da shaidar irin sana’ar da suke gudanarwa da shaidar dan kasa da na karamar hukumna da kuma takardun shaidar bude ausuun banki.”
Kananan masana’antun da suka amfana da bashin naira miliyan 1 za su biya ne a cikin shekara 3 yayin da wadanda suka amfana da naira biliyan 1 za su biya a cikin shekara 5.