Gwamnatin Tarayya ta amince da gina wa alkalai gidaje 40 a Abuja cikin shirin “Renewed Hope Agenda”.
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ne, ya sanar da wannan bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin.
- Shugabannin Tsaro Sun Gaza, Ya Kamata Gwamnati Ta Sake Lale – Farfesa Lugga
- Ofishin Jakadancin Saudiyya Ya Yi Bikin Cikar Daularsu Shekaru 94 Tare Da Karfafa Alaka Da Nijeriya
An tsara gina gidajen ne don samar da wuraren zama masu aminci ga ma’aikatan shari’a, inda aka ware gidaje 20 ga Babbar Kotun Abuja, gidaje 10 ga Babbar Kotun Tarayya, da gidaje 10 ga Kotun Daukaka Kara, duk a unguwar Kantampe.
Wike, ya bayyana cewa aikin za a kammala shi cikin watanni 15, wanda zai magance matsalar alkalai na zaman gidajen haya da otal-otal.
Baya ga gina gidajen, Majalisar Zartarwa ta kuma amince da aikin gina hanyoyi da wasu ababen more rayuwa da wurare masu muhimmanci kamar Kotun Daukaka Kara.
Haka kuma, an amince da wasu ayyukan gine-gine a kauyukan Abuja, inda za a samar da hanyoyi masu tsawon kilomita 75 a Kwali, Gwagwalada, da Bwari.
Gwamnatin ta kuma soke kwangilar da ta bayar a baya na gina Maitama 2 saboda tsaiko da aka samu yayin aikin.