Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bayyana shirinta na kaddamar da bayar da tallafin kudi ga magidanta mutum miliyan 12 don cire su daga cikin yanayin kunci da matsin tattalin arziki da ake ciki.
Ministan Kudi, Wale Edun, ne ya bayyana haka a yayin taron karawa juna sani da ma’aikatarsa ta shirya a garin Uyo na jihar Akwa Ibom a ranar Laraba.
- Tinubu Ba Zai Yi Murabus Ba, inji Ministan Yaɗa Labarai
- Zanga-zangar Tashin Farashin Kayan Abinci Da Matsin Rayuwa Ta Barke A Jihar Oyo
Ministan ya ce shirin an tsara shi ne dan ganin an fara tallafawa magidanta mutum miliyan uku don cire su daga cikin halin kunci da ake ciki, sannan daga baya shirin ya kara yawan wanda za a tallafawa zuwa mutum 12.
“Mun san cewa akwai kusan mutane miliyan 3 da suka amfana a yanzu, amma idan aka yi la’akari da yadda yanayin yake dole zamu zuwa mutane miliyan 12, don suma su ci gajiyar wannan shirin.” Cewar Minista.