Gwamnatin Tarayya na shirin kwashe daliban Nijeriya a Sudan biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin sojojin Sudan da dakarun Rapid Support Forces (RSF) wanda ya yi sanadin rayuka da barnata dukiya a kasar cikin kwanaki biyun da suka gabata, kuma hakan ke barazana ga rayuwar baki.
Hon Abike Dabiri-Erewa, Shugabar hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna ketare (NIDCOM), Acikin wata sanarwa da jami’in hulda da yada labarai Gabriel Odu ya fitar a ranar Alhamis, ta nuna damuwarta kan halin da daliban Nijeriya da ke Sudan ke ciki.
Abike ta bayyana cewa hukumar ta samu takardar neman agajin gaggawa daga kungiyar dalibai ta Nijeriya da ke Sudan musamman ga daliban da ke Khartoum, babban birnin kasar Sudan, NIDCOM ta bada tabbacin cewa, hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) da ke kula da aikin bada agaji, ta fara tuntubar hukumomi da bangarorin da abin ya shafa kan yunkurin fara kwashe daliban da ke kasar.
Don haka ta bukaci daukacin daliban Nijeriya da ke Sudan da kuma ‘yan Nijeriya mazauna Sudan da su kasance cikin lura da sha’anin tsaro cikin kwanciyar hankali.
Rikici ya barke a Sudan ne sakamakon rashin jituwa kan yadda za a shigar da dakarun RSF a cikin sojojin kasar a daidai lokacin da kasar ke shirin kawo sabon mulkin siyasa bayan hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir.