• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Za Ta Muhimmanta ‘Yancin ‘Yan Jarida – Minista

by Sulaiman
2 years ago
Gwamnatin tarayya

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce gwamnati za ta ƙara himma sosai wajen jaddada ‘yancin ‘yan jarida.

Da ya ke jawabi lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), Idris ya ce ‘yancin ‘yan jarida da kafafen yaɗa labarai babban ginshiƙi ne wajen samun nasarar dimokuraɗiyya.

  • Ba A Kafa NBC Don Takura Wa Kafafen Yaɗa Labarai Ba – Minista Idris 
  • Gwamnatin Bauchi Ta Kori Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa Ta Wikki Tourist

Kan haka ne ya ce gwamnati ta himmatu wajen tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida da kafafen yaɗa labarai.

Shugabannin ƙungiyar dai sun kai masa ziyarar ne a ranar Talata, 10 ga Oktoba, 2023.

Ministan ya bayyana manyan ƙalubalen da ‘yan jarida da kafafen yaɗa labarai ke fuskata, waɗanda ya ce sun haɗa da ‘yancin su, samun damar mallakar bayanai da kuma tsaron lafiya da rayukan su.

LABARAI MASU NASABA

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

Ya ce NUJ ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ɗorewar dimokiraɗiyya.

Ya hore su da a haɗa hannu domin samun ci gaba. Ya ce: “Muradin da mu ka sa a gaba shi ne mu tabbatar da cewa ‘yan jarida su na gudanar da aikin su ba tare da fargabar wata barazana ga lafiya ko rayuka ba.”

Sai dai kuma ya yi tsokacin cewa duk da ‘yancin ‘yan jarida abu ne mai matuƙar daraja a fagen yaɗa labarai, to kuma abu ne mai muhimmanci a ga cewa ana yin taka-tsantsan tare da bayar da labarai sahihai ga ‘yan Nijeriya.

Ya jaddada cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da gaske ta ke yi wajen kula da ‘yancin ‘yan jarida, tare da ƙoƙarin ganin sun riƙa gudanar da aikin su ba tare da tsangwama ko wani cikas ba.

A jawabin sa, Shugaban NUJ na ƙasa, Mista Chris Isiguzo, ya fayyace ƙalubalen da ‘yan jarida ke fuskanta, waɗanda su ka haɗa da ‘yancin ‘yan jarida, damar ba su bayanai a ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati, tsaron lafiya da rayukan su da kuma matsalolin na yau da kullum na tsadar rayuwa.

Ya ce ya na yi wa ministan kallon wani nagartaccen tsanin da za a taka domin a kai ƙololuwar wurin da za a iya magance waɗannan matsaloli.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi
Labarai

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

October 19, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza
Labarai

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar
Labarai

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Next Post
Shugabannin Kasashen Duniya Na Cike Da Kyakkyawan Fata Game Da Taron Raya Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya

Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

October 19, 2025
Yadda Ake Alkaki

Yadda Ake Alkaki

October 19, 2025
Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (2)

October 19, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.