Karamin Ministan harkokin jin ƙai da walwalar jama’a, Tanko Sununu, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na shirin raba tallafin kuɗi ga iyalan da ke cikin ƙunci domin rage raɗaɗin talauci a ƙasar nan.
Sununu ya bayyana hakan ne a cikin shirin Sunrise Daily na Channels TV a ranar Litinin, inda ya ce sama da iyalai miliyan biyu da ɗari biyu (2.2m) ne da aka saka a rajistar jin kai za su fara karɓar tallafin kuɗin nan ba da daɗewa ba. Ya ce kafin ƙarshen watan Agusta za a kai ga rabawa waɗannan iyalan tallafin.
- Gwamnatin Tarayya Ta Ba Da Tallafin Kashi 50% Ga Kiristoci Masu Zuwa Ziyarar Ibada A Isra’ila
- MOFA: Batun Taiwan Ba Ya Bukatar Tsangwama Daga Waje
Ministan ya ƙara da cewa ofishin NASSCO ne zai fitar da sunayen waɗanda suka fi rauni a cikin rajistar ƙasa, domin a tabbatar tallafin ya isa ga masu buƙata na gaske. Ya ce a baya an riga an samu ci gaba mai kyau a shirin rabawa Talakawa tallafin kuɗi (Conditional Cash Transfer (CCT) inda aka raba biliyoyin Naira ga talakawa.
“Har zuwa yanzu mun raba Naira biliyan 419 ga ƴan Nijeriya miliyan biyar, inda kashi 71% daga ciki aka rabawa arewacin ƙasa, yayin da kashi 21% ya je kudu,” in ji shi. Sununu ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakai na musamman domin rage matsin rayuwa ga talakawa da maras a galihu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp