Gwamnatin tarayya na shirin yin wasu manyan manyan tituna guda biyu a fadin kasar nan ta hanyar tsarin hadin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu.
Ministan ayyuka, Dave Umahi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa ranar Lahadi bayan wata ganawa da ya yi da shugaban kasa, Bola Tinubu a Abuja.
- Gwamnatin Tarayya Ta Kara Farashin Mitar Wutar Lantarki
- Gwamnatin Tarayya Ta Roki NLC Da Ta Janye Shirin Tsunduma Yajin Aiki
Ya ce manyan hanyoyin za su taso ne daga Abuja zuwa Legas da Fatakwal zuwa Legas, inda ya ce za a samar musu da kayayyakin agajin gaggawa don jin dadin tafiye-tafiye.
Manyan tituna an tsara su ne don yin tafiya cikin sauri, suna da hanyoyi sama da daya a kowane bangare na ababen hawa da layin tsaro da ke raba bangarori biyun.
Ministan ya ce gwamnati ta kulla alkawurra daga masu ruwa da tsaki domin ganin aikin ya samu nasara akan lokaci.
Umahi ya kuma bayyana cewa an yi wa shugaban kasa bayani kan bukatar samar da tsari mai kyau don samar da kudaden gudanar da ayyukan titunan.
Ministan ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa babu wani aiki da gwamnatin da ta shude ta fara da gwamnati za ta yi watsi da shi.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta gaji ayyuka 2,604 da kudinsu ya kai Naira tiriliyan 14 da suka shafi tituna kilomita 18,000, inda ya ce an yi alkawarin biyan tiriliyan hudu daga cikin wannan kudi.
Ministan ya kara da cewa gwamnati ta kuma dukufa wajen yin amfani da ingantaccen simintin da aka don gina tituna a fadin kasar nan.
A ceqarsa ‘Kankare’ yana iya jure nauyin manyan motoci kuma yana daukar tsawon shekaru ana amfani da shi ba tare da fama da gyare-gyare ba.
Dangane da tangardar da aka samu a kan gadar Mainland da Third Mainland, Umahi ya ce an fara aiki kuma an dakatar da ababen hawa da ke zirga-zirga a yanzu haka.