• English
  • Business News
Friday, September 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tinubu Na Ƙoƙarin Gyara Kurakuran Baya, Ba Jawo Wahala Ba – Minista

by Sulaiman
1 year ago
in Labarai
0
Gwamnatin Tinubu Na Ƙoƙarin Gyara Kurakuran Baya, Ba Jawo Wahala Ba – Minista
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce, babban abin da gwamnatin Tinubu ta fi mayar da hankali a kai ba shi ne ta ɗora wa ‘yan Nijeriya wahala ba, sai dai ta gyara munanan tsare-tsare da matakan da ba su dace ba waɗanda a tarihi suka kawo cikas ga ci gaban Nijeriya.

A wata sanarwa da Mataimakin Ministan na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Rabi’u Ibrahim, ya fitar,  Ministan ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Laraba yayin da yake ganawa da jami’an diflomasiyya a Ma’aikatar Harkokin Wajen Ƙasar dangane da zanga-zangar da aka yi a faɗin ƙasar.

  • Gwamnan Gombe Ya Bayar Da Umurnin Raba Kayan Abinci Don Rage Raɗaɗin Kuncin Rayuwa
  • Gwamnatin Filato Ta Sassauta Dokar Hana Fita A Jihar

Ya jaddada ƙudirin Shugaba Tinubu na aiwatar da gyare-gyare da nufin samar da ci gaba mai ɗorewa da kuma inganta rayuwa ga ɗaukacin ‘yan ƙasa, yana mai cewa, ƙalubalen da ake fuskanta a yanzu na wucin-gadi ne.

Labarai Masu Nasaba

Hasashen Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Shirin Ko-ta-kwana

Gwamnan Kebbi Ya Dakatar da Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya Biyo Bayan Sakaci A Aiki

Ministan ya ce, “Yana da muhimmanci mu fara da wannan bayanin cewa, Shugaba Tinubu bai zo ofis don ya jawo wahalhalu ko kuma wahalar da ’yan Nijeriya ba. Ya zo ne don warware matsalolin baya; tare da yunƙurin gyara da yawa daga cikin tsare-tsaren da ba su da kyau da kuma matakan da ba su dace ba da suka kawo mana koma-baya a matsayin mu na ƙasa shekaru da yawa.

Tinubu

“Shugaban Ƙasa ya hau karagar mulki ne a ɗaya daga cikin lokuta mafi ƙalubale a tarihin Nijeriya, inda ƙasar ke kashe kashi 97 na dukkan kuɗaɗen shigarta wajen biyan basussuka; tare da yawaitar talauci, hauhawar rashin aikin yi, lalacewar ababen more rayuwa, da rashin tsaro. Yayin da take fuskantar waɗannan abubuwa masu ban tsoro, gwamnati ta ɗauki ƙwararan matakai tare da aiwatar da gyare-gyaren da aka daɗe ba a yi ba domin ceto tattalin arziƙin ƙasar daga durƙushewa.”

Ministan ya bayyana cewa kawar da tallafin man fetur ya zama dole don karkatar da kuɗaɗen zuwa sassa masu muhimmanci kamar kiwon lafiya, ilimi, ababen more rayuwa, da tsaro, wanda ke tasiri kai tsaye ga jin daɗin ’yan ƙasa da ci gaban ƙasa.

Ya amince da cewa ana shan raɗaɗin sauyin da ke tattare da wannan matakin kuma ya yi nuni da cewa Gwamnatin Tarayya ta tsara shirye-shiryen shiga tsakani don magance waɗannan ƙalubale.

“Mun dage sosai kan tabbatar da cewa an aiwatar da waɗannan ayyukan domin kawo sassauci ga ‘yan Nijeriya,” inji Idris.

Yayin da yake magana kan zanga-zangar da aka gudanar a faɗin ƙasar nan, ministan ya ce gwamnati na mutunta ‘yancin yin taro cikin lumana da ‘yancin faɗin albarkacin baki, waɗanda su ne ginshiƙin dukkan al’ummomin dimokiraɗiyya, amma ya jaddada cewa abin da ya fara a matsayin zanga-zangar lumana a wasu jihohi da kuma Babban Birnin Tarayya shi ne ba da jimawa ba wasu da suka kutsa kai cikin zanga-zangar suka karɓe ragamar tare da shirya tarzomar da ta lalata rayuka da dukiyoyi.

“An samu rahotannin ƙone-ƙone, ɓarna, sace-sace, da kuma arangama da jami’an tsaro a garuruwa da dama. Abin takaici, waɗannan al’amura sun yi sanadin asarar rayukan da ba su ji ba ba su gani ba da kuma asarar dukiya mai yawa,” inji shi.

Idris ya tabbatar wa da jami’an diflomasiyya cewa Gwamnatin Tarayya ta fara gudanar da bincike kan tashe-tashen hankulan da aka yi a lokacin zanga-zangar domin a gano tare da gurfanar da duk masu hannu a cikin lamarin.

Ya ce: “Mun himmatu wajen hana sake aukuwar irin wannan mummunan lamari a nan gaba.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AlmundahanaRashin TsaroTabarbarewar Tattalin ArzikiTsadar Rayuwa
ShareTweetSendShare
Previous Post

Shugaban Timor-Leste Ya Yaba Kayayyaki Kirar Kasar Sin

Next Post

Jami’in Kenya: Taron Dandalin FOCAC Zai Zurfafa Dangantakar Sin Da Kenya

Related

Hasashen Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Shirin Ko-ta-kwana
Labarai

Hasashen Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Shirin Ko-ta-kwana

5 hours ago
Gwamnan Kebbi Ya Dakatar da Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya Biyo Bayan Sakaci A Aiki
Labarai

Gwamnan Kebbi Ya Dakatar da Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya Biyo Bayan Sakaci A Aiki

6 hours ago
Shettima
Labarai

Shettima Ya Bada Umarnin Gaggauta Raba Lamunin Naira Biliyan 250 Ga Ƙananan Manoma 

7 hours ago
Rashin Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jihar Kogi 
Labarai

Rashin Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jihar Kogi 

8 hours ago
Boko Haram Na Yin TikTok, Suna Sarrafa Jirage Marasa Matuƙi Don Sa Ido Kan Sansanonin Soji – Bulama 
Labarai

Ƙwararren Masanin Tsaro, Bulama Ya Ƙaryata Iƙirarin El-Rufai Kan Biyan ’Yan Bindiga Kuɗaɗen Fansa

10 hours ago
Gwamnatin Tarayya Ta Ɓullo Da Kwasakwasai 26 Na Kasuwanci Don Rage Yawan Masu Neman Aikin Gwamnati
Manyan Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Ɓullo Da Kwasakwasai 26 Na Kasuwanci Don Rage Yawan Masu Neman Aikin Gwamnati

11 hours ago
Next Post
Jami’in Kenya: Taron Dandalin FOCAC Zai Zurfafa Dangantakar Sin Da Kenya

Jami’in Kenya: Taron Dandalin FOCAC Zai Zurfafa Dangantakar Sin Da Kenya

LABARAI MASU NASABA

Tattalin Arzikin Sin Babban Ginshiki Ne Na Karuwar Tattalin Arzikin Duniya

Tattalin Arzikin Sin Babban Ginshiki Ne Na Karuwar Tattalin Arzikin Duniya

September 12, 2025
Duniya Za Ta Ci Karin Gajiya Daga Karfafuwar Hadin Gwiwar BRICS 

Duniya Za Ta Ci Karin Gajiya Daga Karfafuwar Hadin Gwiwar BRICS 

September 12, 2025
Hasashen Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Shirin Ko-ta-kwana

Hasashen Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Shirin Ko-ta-kwana

September 11, 2025
Sin Ta Kasance Kan Gaba A Yawan Hakkin Mallakar Fasaha A Bangaren Tattalin Arziki Na Dijital

Sin Ta Kasance Kan Gaba A Yawan Hakkin Mallakar Fasaha A Bangaren Tattalin Arziki Na Dijital

September 11, 2025
Gwamnan Kebbi Ya Dakatar da Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya Biyo Bayan Sakaci A Aiki

Gwamnan Kebbi Ya Dakatar da Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya Biyo Bayan Sakaci A Aiki

September 11, 2025
Za A Gudanar Taron Tattaunawa Karo Na 12 Na Dandalin Xiangshan A Nan Birnin Beijing

Za A Gudanar Taron Tattaunawa Karo Na 12 Na Dandalin Xiangshan A Nan Birnin Beijing

September 11, 2025
Shettima

Shettima Ya Bada Umarnin Gaggauta Raba Lamunin Naira Biliyan 250 Ga Ƙananan Manoma 

September 11, 2025
An Zabi Wuraren Ban Ruwa Hudu Na Kasar Sin Domin Shigar Da Su Jadawalin Wuraren Ban Ruwa Na Kasa Da Kasa

An Zabi Wuraren Ban Ruwa Hudu Na Kasar Sin Domin Shigar Da Su Jadawalin Wuraren Ban Ruwa Na Kasa Da Kasa

September 11, 2025
Rashin Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jihar Kogi 

Rashin Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jihar Kogi 

September 11, 2025
Shawarar Jagorantar Harkokin Duniya: Mafitar Sin Ga Kasa Da Kasa

Shawarar Jagorantar Harkokin Duniya: Mafitar Sin Ga Kasa Da Kasa

September 11, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.