• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tinubu Za Ta Sake Inganta NTA Da FRCN – Minista

by Sulaiman
2 years ago
Tinubu

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙudiri aniyar aiwatar da wasu tsare-tsaren gyara da za su dawo da martabar da aka san mashahuran kafafen watsa labarai biyu ɗin nan da su, wato Hukumar Talabijin ta Nijeriya (NTA) da Hukumar Gidajen Rediyon Tarayya (FRCN).

Hadimin musamman na ministan kan harkokin yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, cewa Ministan ya sha wannan alwashin ne a Kaduna a lokacin da ya kai ziyarar aiki a ofishin hukumomin biyu.

  • Firaministan Cuba: Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Za Ta Amfanawa Duk Duniya
  • Yadda Na Hana ‘Yan Boko Haram Mayar Da Jihar Neja Hedikwatarsu – Tsohon Gwamnan Jihar 

A yayin da ya ke magana kan babbar rawar da gidan Rediyon Tarayya na Kaduna da gidan talabijin na NTA Kaduna su ke takawa wajen jan akalar ra’ayin jama’a da watsa labarai da ɗabbaka musayar al’adu, Ministan ya ce kafafen biyu sun samu koma-baya a ‘yan shekarun nan da su ka gabata saboda watsi da su da aka yi, da rashin tarbiyyar aiki, da tsofaffin wuraren aiki da kayan aiki, wanda hakan ya karya alkadarinsu wajen yin shirye-shirye da taka muhimmiyar rawa.

Ministan ya bada tabbacin cewa, gwamnatin Tinubu za ta farfaɗo da kafafen kuma ta mayar da su kan gaba a aikin rediyo da na talabijin a fadin Nijeriya.

Ya ce: “Yadda za a iya mayar da NTA da FRCN matsayin wakilan ƙwarai a tsare-tsaren Gwamnatin Tarayya sosai, tilas sai mun yi la’akari da babbar gazawarsu a yanzu a fagen da ke cike da gasa, da amfani da basira, da amfani da fasahohin zamani.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

“Dalilin zuwa na nan tare da Darakta-Janar na NTA da na FRCN shi ne, domin mu nemo cikakkiyar hanyar da za mu bi don magance waɗannan matsalolin, wanda ya na kan gaba cikin abubuwan da mu ka ba muhimmanci.

“Za mu duba dukkan zaɓi da ke gabanmu domin tabbatar da cewa mun dawo da martabar da NTA da FRCN su ka rasa.”

Ministan ya ce matsalar FRCN a matakin ƙasa da na jihohi ya ma fi ta’azzara, musamman ma a Rediyon Nijeriya, Kaduna, wanda ya bayyana da cewa “a shekaruj baya, sun kasance wuri ne mai daraja na yaɗa labarai wanda ya samar da zaƙaƙuran ma’aikatan rediyo.

“Hakika, Rediyo Nijeriya Kaduna na buƙatar a farfaɗo da shi da gaggawa. Babu shakka za mu ɗauki mataki da sauri a wannan aiki na ceto,” inji shi.

Idris ya ce a lokacin da ya kama aiki, ya samu kiraye-kiraye masu yawa daga sassa da dama daga masu ruwa da tsaki a kan lalacewar kafafen biyu, ya na mai nanata cewa lallai aikin da ke gabansa shi ne tabbatar da cewa an yi wa NTA da FRCN garambawul domin su cimma manufofin kafa su.

Ya ce: “Ina tabbatarwa shugabanni da ma’aikata da sauran masu ruwa da tsaki a NTA da FRCN cewa, Shugaba Tinubu ya naɗa Malam Salihu Abdulhamid Dembos da Dakta Mohammed Bulama a matsayin Darakta-Janar na NTA da FRCN ne bayan cikakken nazari kan ƙwarewarsu wajen iya kawo kyakkyawan sauyi a hukumomin biyu waɗanda babu hukumomin aikin talabijin da rediyo kamarsu wajen girma a Nijeriya da ma Afrika baki ɗaya.

“A shirye na ke in duba kowace dama da ke akwai wadda za ta bayar da duk abin da ake buƙata don tabbatar da cewa, an sama wa NTA da FRCN kayan aiki na zamani, kuma a baiwa ma’aikatansu cikakkiyar horaswa da kuma biya masu haƙƙoƙin aiki.”

Ministan ya ce ya kamata hukumomin yaɗa labaran biyu su tashi tsaye su rungumi yanayin aikin jarida wanda zamani ya kawo wajen aiki da kayan fasaha na zamani idan har su na so a yi gogayya da su, su inganta kyawun aiki, kuma sakonni su su kai ga ɗimbin masu kallo da masu saurare.

A lokacin ziyarar, Ministan da tawagarsa sun duba muhimman kayan aikin tashoshin biyu da ke cikin garin Kaduna da kuma garin Jaji a babban titin Kaduna zuwa Zariya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140
Labarai

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Majalisar Dattawa
Labarai

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa
Labarai

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Next Post
Shugaba Xi Ya Yi Kira Da A Ingiza Muhimmiyar Rawa Da Tsarin Mulkin Kasa Ke Takawa A Fannin Jagorancin Kasa

Shugaba Xi Ya Yi Kira Da A Ingiza Muhimmiyar Rawa Da Tsarin Mulkin Kasa Ke Takawa A Fannin Jagorancin Kasa

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.