Gwamnatin Jihar Zamfara, karkashin jagorancin gwamna Dauda Lawal, ta bayyana shirinta na hadin gwiwa da kasar Sweden a bangarori daban-daban da suka hada da hakar Ma’adanai, Noma, Makamashi, Ilimi da Kiwon lafiya a Jihar.
Babban mataimaki na musamman na Gwamnan kan harkar yada labarai, Sulaiman Bala Idris ne ya bayyana hakan a wata takarda da ya sanya wa hannu aka rabawa manema labarai.
- Durƙushewar Darajar Naira: Atiku Ya Ba Da Mafita Bayan Ya Caccaki Tinubu
- BUA Ya Sanar Da Ƙarawa Ma’aikatansa Albashi Kashi 50 Cikin 100 Saboda Tsadar Rayuwa
Gwamna Lawal ya tabbatar da hakan ne yayin da ya karbi bakuncin jakadiyar kasar Sweden a Nijeriya ne, Annika Hahn-Englund a ofishinsa da ke Abuja.
Idris ya kara da cewa, Gwamna Lawal ya kuduri aniyar binciko duk hanyoyin da za a bi don jawo masu saka hannun jarin kasashen waje da tallafi daga abokan hulda na kasa da kasa da kuma na cikin gida.
Gwamna Lawal ya tabbatar wa Jakadar kasar Sweden cewa, a shirye Gwamnatinsa ta ke na inganta hadin gwiwa da ci gaba mai dorewa a bangarori daban-daban.
Anata jawabin, jakadar ta yi alkawarin baiwa jihar Zamfara goyon baya a fannin hako ma’adanai, dabarun noma na zamani, samar da makamashi dan tallafawa wajen inganta harkokin ilimi da kiwon lafiya.