Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima a ranar Talata ya ce idan aka zabe su a kan karagar mulki a zaben 2023 mai zuwa, gwamnatinsu za ta kawar da talauci a kasar baki daya.
Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana a madadin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu a wajen kaddamar da manhajar gangamin tara wa Tinubu/Shettima kudin yakin neman zabe ta manhajar amfani da wayar salula a Legas.
Ya ce, da wannan manhaja, babu wani dan Nijeriya da za a bar shi a baya wajen bayar da gudunmawar kudi ga yakin neman zaben da duk abin da zai iya bayarwa.
Jam’iyyar na neman gudunmawar Naira biliyan 5 don yakin neman zaben ta.