Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta mika ta’aziyyarta ga jama’a da gwamnatin jihar Zamfara kan rasuwar mutane shida da fashewar wani abu ta rutsa da su a cikin mota a jihar.
Kungiyar, a cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun shugabanta, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara, ta ce lamarin da ‘yansanda suka dora alhakinsa kan kungiyar ta’addanci ta Lakurawa, wani yunkuri ne na kara jefa al’ummar jihar cikin wani mawuyacin hali.
- Afirka Ta Kudu Za Ta Fara Bai Wa ‘Yan Nijeriya Bizar Shekaru 5
- Allah Ya Yi Wa Mawaƙin Kannywood, El-Mu’az Birniwa Rasuwa
Sanarwar ta ce: “Muna yin Allah wadai da wannan harin ta’addancin, kuma muna kira ga sojojin Nijeriya da su kara himma wajen ganin sun murkushe wadannan ‘yan ta’adda, masu aikata laifuka a kasarmu,” in ji kungiyar a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.
NGF na mika ta’aziyya ga Gwamna Dauda Lawal da iyalan wadanda abin ya shafa, tare da addu’ar Allah ya sanya Aljannah ce makoma ga wadanda lamarin ya rutsa da su.