Gwamnonin Arewa-maso-Gabas sun bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya ba da fifiko kan sake dawo da ayyukan hakar mai a rijiyoyin Kolmani da tafkin Chadi a wani bangare na kokarin farfado da tattalin arzikin yankin da kuma rage rashin tsaro.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, wanda ya yi magana a madadin takwarorinsa a ziyarar da suka kai wa shugaban kasa a fadarsa da ke Abuja a ranar Laraba, ya ce, ci gaba da hako man a rijiyoyin zai sake taimaka wa ayyukan soji da kuma habaka ci gaban yankin.
- Firaministan Senegal: Yadda Sinawa Ke Girmama Tarihi Da Kiyaye Labarun Abubuwan Da Suka Faru Da Su Na Da Matukar Burgewa
- Sin: Bin Tafarki Na Gaskiya
Zulum ya yaba wa Tinubu kan yadda ya ci gaba da yaki da ta’addanci da kuma yadda ya taimaka wajen dakile illolin ambaliyar ruwa da kwararowar hamada da sauran kalubalen muhalli, inda ya ce yankin ya sha fama da koma bayan muhalli.
Gwamnonin, a yayin da suke karin haske kan manufofin sabunta fata na shugaban kasa kan samar da abinci da cewa, ya kamata a bayar da kulawa ta musamman ga dazuzzukan da ba bu dan adam, sahara, kwazazzabai da koguna da suka zama maboyar ‘yan tada kayar baya.
Dangane da batun tsaro, gwamnonin sun bukaci a ci gaba da gudanar da ayyukan soji a wuraren da suka hada da gabar tafkin Chadi, Dajin Madama, tsaunin Mandara, dajin Sambisa, yankunan Mansur, Yelwa, Futuk, Kolmani, dajin Karin Lamido da sauran wurare a yankin Arewa maso Gabas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp