Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas (NEGF) ta nuna damuwa game da kwararar ‘yan bindiga a wasu jihohin yankin.
Damuwar na kunshe ne a cikin wata sanarwar da aka fitar a taron da aka kammala karo na 8 na kungiyar a Maiduguri, wanda shugaban kungiyar, Gwamna Babagana Zulum ya sanya wa hannu.
- Gwamnonin Arewa Maso Yamma Sun Gana Da Tinubu Kan Matsalar Tsaro
- Matsalar Tsaro: Gwamnonin Neja Da Zamfara Sun Tattauna Da Ribadu
Taron wanda ya bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta shiga tsakani, ta ce ‘yan bindigar su ne wadanda sojoji suka fatattake su a wasu sassan kasar nan, inda a yanzu suka koma yankin, musamman jihohin Bauchi, Gombe da Taraba.
Kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sa baki cikin gaggawa don magance matsalar.
Majalisar gwamnonin ta na sane da cewa wasu sarakunan gargajiya da wasu kananan hukumomi suna hada kai da ‘yan bindigar, suna ba su mafaka da fakewa domin aikata laifuka a yankin.
Sanarwar ta kara da cewa, taron ya yanke shawarar daukar tsatsauran mataki ga duk wani basaraken gargajiya ko shugaban al’umma da aka samu yana hada baki da ‘yan fashin dajin,” Cewar sanarwar.