Gwamnonin Arewa Maso Gabas sun fara taron kungiyar gwamnonin, a karo na 11, wanda aka fara da kimanin karfe 11:00 na safiyar ranar Alhamis, a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Taron ya samu halartar gwamnonin yankin da suka hada da Ahmad Umar Fintiri, Adamawa; Farfesa Babagana Umara Zulum, Borno da mataimakin Gwamna, Hon. Auwalu Jatau, Bauchi.
- Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Ya Nuna Gazawar Gwamnatin Trump Kwanaki 100 Bayan Kama Aiki
- Mutum 20,000 Sun Nemi Gurbin Aikin Mutum 4,000 Cikin Kwana Ɗaya A Adamawa
Sa’ilin da yake jawabi kan taron, shugaban kungiyar gwamnonin yankin, kuma Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jaddada bukatar daukin gaggawa wajen magance matsalolin da yankin ke fuskanta, musamman a fannonin karancin abinci, tabarbarewar harkokin sufuri, kiwon lafiya, sannan uwa uba, koma bayan tattalin arziki.
Gwamnan Zulum ya yi tsokaci dangane da yadda tabarbarewar harkokin tsaro ke ci gaba da zafafa a yankin, yayin da kuma ya yaba wa kokarin sojojin Nijeriya, inda ya ce, “Ina kira gareku, ku ci gaba da yaki da yan ta’adda har sai mun kawo karshen wannan matsalar.”
“Dawowar hare-haren yan ta’adda a cikin jihohinmu wani al’amari ne mai matukar tayar da hankali wanda hakan zai iya wargaza nasarorin da aka samu a fagen yaki da matsalolin tsaro a yankin. Ina mai bayar da shawarar cewa, sojojinmu su fadada sabbin dabarun da suke dasu wajen dakile farmakin yan ta’adda.”
Gwamna Zulum ya ce, “kangin talaucin da yankinmu yake fuskanta, abin tsoro ne, kuma ya zama dole mu dauki ingantattun matakai don magance wannan kalubale. Mu fahimci cewa talauci babbar barazana ne ga tattalin arziki, wanda zai iya shafi zamantakewa.”
“A kokarin nemo madafa, noma kadai ba zai kasance mafita ba, a yaki da talauci. Dole mu kara mayar da hankali kan samar da kyakkyawan yanayi don kafa kananan da matsakaitan masana’antu a yankin mu.”
“Abin ya hada da sa hannun jari a kayayyakin more rayuwa, bayar da fifiko wajen zuba jari mai yawa ga kamfanoni masu zaman kansu, don habaka kasuwanci da kirkire-kirkire.”
Ya ce dole ne su yi aiki don rage talauci ta hanyar samar da ayyukan yi, bunkasa tunani tare da tallafa wa kananan masana’amtu, bunkasa kasuwanci, ta fuskar habaka masana’antu, don fadada tattalin arziki tare da samar da dama ga matasa.
Da farko, mai masaukin bakin taron, kuma Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, a lokacin da yake jawabin bude taron, ya ce a matsayinsu na Gwamnonin yankin za su yi amfani da dandamalin wajen yanke shawarar da za ta kai ga samar da mafita ga matsalolin da yankin yake fuskanta.
“Irin karfin niyya da kyakkyawan kudurori, shawara mai nagarta, da daukakar mataki a cikin gaggawa, wanda shugabanin mu da suka gabata, ko shakka babu sun haskaka makomar yankin Arewa Masu Gabas.
“Yau ma gashi mun taru domin daukar sabbin kudurori da shawarwari nagari, don bin sawun magabatanmu wajen kawo ci gaba a yankinmu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp