Batun kafa Rundunar Ƴan Sanda mallakar gwamnatocin jihohi ya dade yana ɗaukar hankalin al’umma, inda ake tafka muhawara kan alfanu da rashin alfanun ƙirƙiro da jami’an da manufarsu ita ce taimakawa wajen kawar da matsalolin tsaro da suka ƙi ƙarewa.
Masu ruwa da tsaki sun buƙaci kafa ƴan sandan jihohi ne saboda yadda taɓarɓarewar sha’anin tsaro a yankin Arewa ya kai ƙololuwar mataki, ta yadda ƴan ta’adda ke cin karen su ba babbaka ta hanyar yi wa al’umma kisan ƙare dangi, garkuwa da mutane, ƙone garuruwa, sanya dubun-dubatar jama’a gudun hijira da hanawa ɗimbin al’umma noma. Rahoton ƙididdigar 2024–2025 ya nuna Rundunar Ƴan Sanda a Nijeriya na da jami’ai dubu 370,000 tare da shirin ɗaukar ƙarin jami’ai dubu 30,000 a kowace shekara zuwa shekaru shida, domin a kai ga ƴan sanda 650,000 a faɗin ƙasa. Sai dai adadin yawan ƴan sanda a Nijeriya ya saɓa da shawarar Majalisar Ɗinkin Duniya na aƙalla jami’i ɗaya ya riƙa kula da mutane 450.
- Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi
- Tinubu Ya Bayar Da Umarni Karya Farashin Kayan Abinci A Nijeriya
Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa kafa ƴan sandan jihohi ba zaɓi ba ne, wajibi ne domin ceto rayukan al’umma da dukiyoyinsu daga hannun makasa. A kwanan nan Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta tabbatar da cikakken goyon bayanta ga kafa Rundunar Ƴan Sanda a jihohi a matsayin mataki na kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta dabaibaye yankin Arewa. Kakakin ƙungiyar, Gwamnan Gombe Muhammad Inuwa Yahaya, ya ce Gwamnonin Arewa 19 sun amince a kafa ƴan sandan jihohi tare da haɗa su cikin sauran hukumomin tsaro wajen kawar da matsalolin tsaron ƙasa.
Sai dai, masana tsaro da ƙungiyoyin dattawa sun yi kashedi kan yiwuwar wasu gwamnoni su yi amfani da rundunar don muzgunawa abokan adawa. Farfesa Tukur Baba ya nuna damuwa kan batun kuɗin gudanarwa da yiwuwar biyan albashi, yana tambaya: “Mene ne zai faru idan aka kasa biyan jami’an da ke riƙe da makamai?” Tsohon Sufeto Janar na ƴan sanda Mike Okiro ma ya bayyana cewa kafa ƴan sandan jihohi ba shi ne mafita ba, yana mai jaddada cewa matsalar tsaro a Nijeriya ta samo asali ne daga ƙarancin kuɗi, kayan aiki da jami’ai.
A gefe guda, wasu shugabanni sun yaba da wannan mataki. Ƙungiyoyi kamar Dattawan Arewa, ACF, da Afenifere sun bayyana goyon bayansu, suna mai cewa kafa ƴan sandan jihohi na da matuƙar muhimmanci a wannan lokaci. Sai dai wasu, kamar tsohon Sanata Shehu Sani da Anthony Sani, sun nuna cewa akwai barazanar amfani da rundunar wajen cimma muradun siyasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp