Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) ta yi kakkausar suka kan harin da aka kai Makarantar Ƴan Mata ta Gwamnati (GGCSS) da ke garin Maga a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi, wanda ya kai ga sace ɗalibai da dama tare da kashe wasu jami’ai.
Da ya ke tsokaci kan wannan mummunan lamari ta cikin sanarwar da Malam Ismaila Uba Misilli, Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe ya fitar, shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
- Sin: Ya Zama Wajibi A Dakile Mummunan Yanayin Wanzuwar Tashe-tashen Hankula Da Yunwa
- Wani Mai Taɓin Ƙwaƙwalwa Ya Kashe Soja A Legas
Gwamna Inuwa ya kuma ce sace yaran rashin hankali ne da ba za a amince da shi ba, tare da bayyana cewa ci gaba da kai hare-hare a makarantu yana babbar barazana ga zaman lafiyan Arewa da makomar ilimi a ƙasar nan.
Gwamna Inuwa Yahaya, a madadin takwarorinsa na ƙungiyar, ya jajantawa gwamnati da al’ummar Jihar Kebbi musamman iyalan ɗaliban da aka sace da kuma waɗanda suka rasa rayukansu a harin.
Ya kuma bai wa Gwamna Nasir Idris na Jihar ta Kebbi tabbacin haɗin kai da goyon bayan ƙungiyar a wannan mawuyacin lokaci.
Gwamna Yahaya ya ce dole ne makarantu su zama wuraren koyo, ba wai wuraren tashin hankali ba, yana mai gargaɗin cewa ci gaba da kai hare-hare kan cibiyoyin ilimi yana barazana ga nasarorin da aka samu wajen inganta harkokin karatu a makarantu da kuma daƙile matsalar yaran da basa zuwa makaranta a yankin.
Ya nuna matuƙar damuwa kan irin halin da ƴan matan makarantar da aka sacen ke ciki, ya kuma yi ƙira da a gaggauta gudanar da wani shiri na haɗin gwiwa da jami’an tsaro don ganin an ceto su da kuma kama waɗanda suka aikata laifin.
Da ya ke jaddada ƙudurin ƙungiyar gwamnonin na Arewa na haɗa kai da gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro, Gwamna Yahaya ya bayyana cewa, tsaro, ilimi da walwalar matasan Nijeriya na ci gaba da zama babban muradin ƙungiyar.
Shugaban ƙungiyar ta gwamnonin Arewa ya yi addu’ar Allah ya dawo da ‘yan matan makarantar da aka sace da wuri lafiya, ya kuma jajantawa iyalan waɗanda abin ya shafa, tare da yin ƙira ga al’umma su kasance cikin shiri da haɗin kai da jami’an tsaro a ƙoƙarin da suke na kawar da miyagun laifuka a yankin.














