Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana alhininsa bisa rasuwar Sarkin Zuru na Jihar Kebbi, Manjo Janar Muhammadu Sani Sami (Gomo II), wanda ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.
Inuwa Yahaya ya bayyana marigayi Sarkin a matsayin shugaba mai kishin ƙasa, dattijo nagari da ya yi fice a aikin Soja da kuma matsayinsa na basarake.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Miƙa Aikin Titin Koko-Zuru Ga Jihar Kebbi
- “Ne Zha 2” Ya Zama Fim Din Kasar Sin Na Farko Da ya Samu Zunzurutun Kudi Yuan Biliyan 10
Ya tuno da rawar da marigayin ya taka a matsayin tsohon Gwamnan Soja na Jihar Bauchi da irin gudunmawar da ya bai wa ci gaban Arewa da Nijeriya baki ɗaya.
Ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan gidan Sarautar, da masarautar Zuru da al’ummar Jihar Kebbi, tare da addu’ar Allah ya jiƙansa ya kuma saka masa da Aljannar Firdausi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp