Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin cikinta game da ambaliyar ruwan da ta auku a yankunan Yola ta Arewa da Yola ta Kudu a Jihar Adamawa.
Ambaliyar ta hallaka mutane da dama, tare da lalata gidaje da dukiyoyi, sannan ta tilasta wa mutane barin muhallansu.
- An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025
- Kotun Ta Ci Tarar Hukumar NYSC Kan Haramtawa ‘Yan Bautar Ƙasa Mata Sanya Siket Da Tauye Musu ‘Yanci
A cikin wata sanarwa, shugaban ƙungiyar, Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na Jihar Kwara, ya ce ƙungiyar tana tare da al’umma da gwamnatin Adamawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri.
Ƙungiyar ta kuma yaba wa ƴansanda da sojoji bisa saurin tura jami’an ceton ruwa domin taimaka wa waɗanda ambaliyar ta shafa.
Gwamnonin sun yi alƙawarin bayar da gudunmawa domin tallafa wa jihar wajen shawo kan wannan matsalar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp