Stanbic IBTC, ya lashe kyautar gwarzon Bankin Shekara ta 2024, saboda jajircewarsa wajen inganta ayyuka bisa tsarin da duniya ke kai, da kyautata alaƙarsa da abokan hulɗa da gudunmawar da ya ke bayarwa wajen bunƙasa tattalin arziƙi a Nijeriya, inda ya yi fice a fannin zuba jari da kasuwanci da haɓɓaka aikin noma.
Wasu daga cikin muhimman nasarorin da bankin ya samu a shekarar 2024 sun haɗa da yin fice wajen jan ragamar janyo hankalin masu zuba hannun jari daga ƙasashen waje a Nijeriya, wanda kusan kashi 30%, na dalar Amurka da aka shigo da ita a farkon rabin shekarar 2024 ta hannun bankin suka shigo, duk da irin kalubalen tattalin arzikiarziki da ake fuskanta.
- Bankin Zenith Ya Tallafa Wa Matasa Da Naira Miliyan 77 A Jihar Legas
- Babu Gudu Ba Ja Da Baya Wajen Yaki Da Hauhawar Farashin Kayayyaki – CBN
Bankin ya taka wani babban mataki, inda darajar da ƙimar kadarorinsa ta zarce Naira tiriliyan ɗaya, tare da riƙe kambun amanar abokan ciniki da hulɗa, a watan Satumbar 2024 jimillar kadarorin bankin sun ƙaru da kashi 41.2%, wanda ya kai Naira tiriliyan 7.263, daga Naira tiriliyan 5.145 na ƙarshen shekarar 2023.
Ribar da bankin ya samu ta ƙaru zuwa Naira biliyan 222.93 a watan Satumbar 2024, hakan wata gagarumar nasara ce mai girma, inda masu saka hannun jarin suka ci gajiyar ribar mai yawa a sakamakon irin jajircewar banki wajen samar da riba a hannun jari.
Ƙarfafa ƙananan masana’antu musamman a fannin harkokin noma, da jari don sassauƙa aikin gona tun daga shuka har zuwa girbi, wannan yunƙurin ya yi dai-dai da manufofin gwamnatin Nijeriya wajen ƙoƙarin rage dogaro da shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje.
Stanbic IBTC ya samar da ci gaba a fannin fasahar zamani da buɗe kafofin da za su zama mafita wajen sauƙaƙa harkoki tsakanin abokan hulɗa da banki wajen samar da inganci da aminci a hulɗa da banki, ta yadda ba lallai sai abokan hulɗar sun ta yin zarya a hanya banki don magance wata matsala.
Bankin ya ƙaddamar da wani shiri mai suna “Together4ALimb” don tallafawa yaran da suka rasa gaɓoɓinsu da ba su kulawa ta musamman, a bangare guda kuma ya fitar da wasu tsare-tsare na tallafin karatu da shirye-shiryen ɓunƙasa tattalin arziki da saka hannun jari a ɓangaren ilimi da wasanni da lafiya da kuma fannin fasaha.
Gwanancewa da irin jajircewar Bankin Stanbic IBTC, da irin sadaukar da kai wajen inganta ci gaban tattalin arziki, ya tabbatar da matsayinsa na zama banki na farko wajen zuba hannun jari a Nijeriya don amfana da riba.