Jaridar LEADERSHIP ta zaɓi kamfanin AVSATEL a matsayin gwarzon shekara ta 2024, saboda gagarumar gudummawar da ya bayar wajen samar da tsaro da aminci a sararin samaniya da kula da zirga-zirgar jiragen sama da kawo ci gaban samar da kayayyakin cikin gida Nijeriya.
AVSATEL, kamfanin cikin gida Nijeriya ne mai kula da zirga-zirgar jiragen sama, ya kawo sauyi a fannin zirga-zirgar jiragen sama a Nijeriya ta hanyar yin amfani da tauraron dan adam mai sauri da tsarin sanya ido cikin hanzari kan yanayin sararin samaniyar ƙasa.
- Kano Ta Kaddamar Da Cibiyar Tafi-da-gidanka Ta Farko A Nijeriya Don Yi Wa Motoci Lasisi
- Za A Shafe Kwanaki Uku Ana Zabga Ruwa Da Tsawa Daga Lahadi – Hasashen NiMet
Bayan da Nijeriya ta fuskanci jarabawa a sararin samanya, ciki har da hatsarurrukan jiragen Sosoliso da ADC, gwamnatin Nijeriyar ta bai wa kamfanin AVSATEL amana don bayar da tsaro da ɗaukaka darajar kayayyakin aikin sufuri a ƙasar. AVSATEL ya amsa kira tare da fara inganta na’urorin sufuri a manyan filayen jiragen sama na Abuja da Legas da Fatakwal da kuma Kano, sai kuma aikin filayen jiragen sama na Birnin Kebbi da Lafia. Ta hanyar waɗannan ayyukan, AVSATEL ya samar da kyakkyawan yanayi mai aminci a sararin samaniyar Nijeriya, tare da ingantattun tsare-tsare waɗanda ke ƙara tabbatar da ci gaba da sa ido kan zirga-zirgar jiragen sama.
AVSATEL bai tsaya a fagen fasaha kadai ba, ya taka rawar gani wajen samar da kayayyakin aiki don ɗorewar hanyoyin sufurin jiragen sama a Nijeriya. Ɗaya daga cikin ci gaba da AVSATEL ya samar, shi ne samar da wuri don sayar da kayan aiki da gyare-gyare na na’urorin sufuri a Abuja, wanda hakan ya bayar da damar yin gyare-gyare da sauri ba tare da jira har sai an sayo wani kayan gyara daga ƙasashen waje ba. Wannan wuri ya bayar da gudummawa matuka wajen rage ɓata lakacin gyara tare da tabbatar da cewa an samar da muhimman abubuwan da za a iya amfani da su nan take.
AVSATEL ya yi nasarar samar da ƙwararru a fannin jiragen sama na Nijeriya, ta hanyar samar da shirye-shiryen horaswa na kamfanin, ya bai wa ɗaruruwan ƙwararru masana harkokin sufurin jiragen sama na Nijeriya fasahar zamani, inda yanzu suke zama a matsayin jagorori a ɓangaren kula da sararin samaniya. Hadin guiwar AVSATEL tare da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa daga Faransa da Koriya ta Kudu da Finland da kuma Austria sun bayar da damar horar da ma’aikata a Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Nijeriya (NAMA), da Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NIMET).
Kamfanin na AVSATEL ya kuma ƙara mayar da hankali wajen horar da ma’aikata kashe gobara don ƙara bunƙasa ɓangaren sufurin jiragen sama don bayar da agajin gaggawa. Kamfanin ya samar da shirye-shiryen horo na musamman ga ma’aikatan kashe gobara. Wannan tunani na bayar da horo ga ma’aikatan ya nuna irin kishi da himmar AVSATEL wajen tabbatar da cewa bai tsaya ga tsaron sararin samaniyar Nijeriya kaɗai ba, har ma da kiyaye rayuwar al’umma da matafiya a duk faɗin ƙasar.
Saboda ficen da kamfanin ya yi, ya samu takardar shaida ta ISO 2001-2015 daga Hukumar Kula da Ƙayayyakin Amfani ta Nijeriya (SON). AVSATEL ya fito da irin cikakken shiri mai inganci da bangaren sufurin jiragen sama na Nijeriya ke da shi.
Kamfanin ya shafe fiye da shekaru ashirin yana tabbatar da nutsuwa da aminci a cikin zukatan matafiya na cikin gida da na ƙetare a yayin gudanar da tafiye-tafiyensu da zirga-zirga a sararin samaniyar Nijeriya.