ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi

by Leadership Hausa
3 weeks ago
Banki

Lokacin da Dr Tony Okpanachi ya shiga ofis a shekarar 2017 a matsayin Shugaban Gudanarwa na farko da Babban Jami’in Zartarwa na Bankin Ci Gaban Nijeriya (DBN), kaɗan ne suka yi tsammanin yadda wannan ƙungiyar za ta zama matattarar tallafi ga dubban ƙananan kamfanoni cikin sauri.

Bayan shekaru takwas, DBN ta tsaya a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu sahihanci wajen haɓaka ci gaban haɗaka a Nijeriya, yana canza rayuka ta hanyar samar da damar samun kuɗi da tallafin ƙwarewar kasuwanci.

  • Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI
  • Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

A tsakiyar wannan sauyi akwai jagora wanda ke ganin banki ba kawai kasuwanci ba ne, har ma a matsayin ayyukan al’umma wata hanya ce ta haɗa manufofi da damar cimmu su.

ADVERTISEMENT

“Aikinmu shi ne tallafa wa mafarkai waɗanda ke gina ƙasa.”

 

LABARAI MASU NASABA

Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

Ƙarfafa Ginshiƙin Tattalin Arziki

A ƙarƙashin jagorancin hangen nesa na Dakta Okpanachi, DBN ta bayar da sama da Naira tiriliyan 1.1 a matsayin lamuni ga fiye da MSMEs 700,000 a faɗin Nijeriya.

Abin da ya sa waɗannan lambobin suka zama na musamman shi ne labarin ɗan’Adam da suke bayyana: Kashi 65 cikin ɗari na masu amfana mata ne da matasa,

Kuma tallafin ya ƙirƙiri ko ya tabbatar da kimanin ayyukan yi miliyan 1.2 a ƙasa baki ɗaya.

Waɗannan ba lambobi ne kawai ba; Labarai ne na  maɗinka a Aba, masu sarrafa shinkafa a Kebbi, masu ƙirƙirar fasaha a Legas, da masu sana’o’i a Kaduna waɗanda yanzu za su iya gudanar da kasuwanci mai ɗorewa saboda wani ya yarda da basirarsu.

Falsafar jagoranci ta Dakata Okpanachi tana da sauƙi: ingancin samun kuɗi shi ne igancin ƙasa. Ta hanyar ƙarfafa MSMEs, ginshikin gaskiya na tattalin arzikin Nijeriya, ya taimaka wajen yaɗa arziki zuwa wurare da bankunan gargajiya da a da can ba sa kula da su ba.

 

Gina Banki Don Ci Gaba, Ba Domin Dogaro Da Tallafi Ba

Dakta Okpanachi ya kawo tsari, ladabi, da manufa mai bayyana: ya sanya DBN zama misali wajen tallafin ci gaban kasuwanci a Afirka.

Ya gabatar da samfurin bayar da lamuni mai amfani da bayanai da fasaha, wanda ke ƙara gaskiya, rage haɗarin bashi, da faɗaɗa damar samun kuɗi ga sassa da ba a kulawa da su sosai. Ta hanyar haɗin gwiwa da cibiyoyin kuɗi fiye da 65, yanzu DBN na ba da tallafin kuɗi mai rahusa da tsawon lokaci ga ƙananan kasuwanci a kowace jiha.

Wannan samfurin ya sami girmamawa a duniya, inda ya sanya DBN zama mai ba da kuɗi kuma malamin banki wanda ke ƙarfafa tsarin kuɗi maimakon yin gogayya da shi.

“Ba mu zo don mamaye kasuwa ba; mun zo ne don zurfafa ta.”

 

Ƙirƙire-Ƙirƙire a Matsayin Dabarun Ci Gaba

Lokacin shugabancin Dr Okpanachi sai ya zama ya cika da ƙirƙire-ƙirƙire, ba wai a kalmar jan hankali kawai ba, har ma da tsarin aiki.

Ya jagoranci ayyukan sauyin dijital da ke ba bankuna da cibiyoyin micro-finance masu haɗin gwiwa damar sarrafa lamunin MSMEs cikin inganci, tare da sa ido kan tasirinsu a lokaci na ainihi.

Haka kuma, ya ƙaddamar da Tsarin Gudanar da Muhalli da Al’umma  na DBN, wanda ke tabbatar da cewa kowanne aikin da aka tallafa ya dace da manufofi masu ɗorewa, daga makamashi mai sabuntawa, zuwa kamfanonin da mata ke jagoranta, da aikin noma mai ɗorewa.

A fannin yabo ga waɗannan nasarori kuwa, abokan haɗin gwiwa na duniya ciki har da Bankin Duniya, da AfDB, da Bankin Zuba Jari na Turai sun faɗaɗa haɗin gwiwar su da DBN, suna yabawa da gaskiyar shugabanci da ƙwarewar gudanarwa.

 

Ɗangaren ɗan’Adam na Harkar Kuɗi

Baya ga lambobi, akwai sadaukarwar Dr Okpanachi wajen gina mutane, ba kawai jadawalin kuɗi ba.

A ƙarƙashin kulawarsa, Shirin Horar da ‘Yan Kasuwa na DBN (Entrepreneurship Training Programme – ETP) ya horar da fiye da ‘yan kasuwa 9,500 da ƙwarewar aiki a fannin haɓaka kasuwanci, shugabanci, da ilimin kuɗi.

Masu kammala shirin ETP sun ci gaba da ƙirƙirar ayyukan yi, samun tallafin kuɗi, da gina kamfanoni masu ɗorewa, suna nuna cewa haɓaka ƙwarewa yana da muhimmanci kamar samun kuɗi.

Ta wannan haɗin gwiwar kuɗi da jagoranci, DBN ta zama banki kuma aji, wurin da kasuwanci ke haɗuwa da ƙarfafawa.

 

Tafiyar Ladabi Da Hangen Nesa

Duk da cewa fiye da shekaru 30 na ƙwarewa a harkar banki wanda ya haɗa kasuwanci, sayarwa ga jama’a, da bankin ci gaba, Dr Okpanachi ya haɗa ƙwarewar fasaha da hankalin ɗan’Adam cikin ƙwarewa ta musamman.

Kafin shiga DBN, ya riƙe manyan muƙamai a Zenith Bank da Bank of Industry, inda ya ƙware wajen gina cibiyoyi da jagorancin dabaru.

Ya samu digiri daga Jami’ar Ahmadu Bello da Jami’ar Legas, har ma da PhD a Fannin Gudanar da Kasuwanci (Business Administration).

Mai kammala karatu daga Harɓard Business School da Alliance Manchester Business School, shi ma’aikaci ne na Chartered Institute of Bankers of Nigeria (CIBN) kuma mai tasiri a cikin al’ummar bankin ci gaban Afirka.

Labarinsa shi ne na mai sauƙin gyara tsarin da ya sami damar yin tasiri a ƙasa baki ɗaya ba tare da yin hayaniya ba.

 

Gado Na Ci Gaba Mai Ɗorewa

A ƙarƙashin jagorancin Dr Okpanachi, DBN ta zama ginshiƙi a tsarin tallafin kuɗi ga MSMEs na Nijeriya — cibiyar misali wacce ke haɗa riba da manufa.

Juriya da ta nuna a lokacin girgizar tattalin arziki, annobar duniya, da rashin tabbas na kuɗaɗen gwamnati ya nuna tsayuwarsa kan ingantaccen shugabanci da tsare-tsaren dogon lokaci fiye da ganin abubuwa na ɗan lokaci.

Yanzu, jadawalin kuɗi na DBN ba a auna shi ne kawai a Naira da Kobo kawai ba, an ma farfaɗo da rayuka, kasuwancin da aka farfaɗo da su, da al’ummomin da aka ƙarfafa.

“Ci gaban ƙasa ba kalma ce kawai ba, shi bambanci ne tsakanin rayuwa yin samun ɗinbin nasara.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola
Manyan Labarai

Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

November 15, 2025
Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa
Manyan Labarai

Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

November 15, 2025
Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70
Da ɗumi-ɗuminsa

Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70

November 14, 2025
Next Post
Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya

Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya

November 15, 2025
Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

November 15, 2025
Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

November 15, 2025
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

November 15, 2025
Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari

Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari

November 15, 2025
Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

November 15, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi

November 15, 2025
Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

November 14, 2025
NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026

NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026

November 14, 2025
NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano

NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano

November 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.