OPay ya samu lambar yabo ta Jaridar Leadership ta kamfani mafi ƙwazo wajen sauƙaƙa mu’amalar kuɗaɗe ta wayar salula da yanar gizo a shekara ta 2024, saboda ƙoƙarin kamfanin na bai wa miliyoyin ‘yan Nijeriya damar faɗaɗa hanyoyin bunƙasa tattalin arziƙi, musamman ga marasa amfani da banki da waɗanda ke samun ƙalubale da bankuna a Nijeriya.
OPay ya taka rawar gani kuma ya yi fice a Nijeriya, don ya zama zakaran gwajin dafi wajen tabbatar da aminci da tsaron kuɗaɗe da sauƙaƙa mu’amala da abokan hulɗa tare da inganta tattalin arziƙin kuɗi a Nijeriya.
- Opay, Palmpay, Kuda Da Moniepoint, Za Su Ci Gaba Da Karɓar Sabbin Kwastomomi Daga Watan Yuli
- Babu Gudu Ba Ja Da Baya Wajen Yaki Da Hauhawar Farashin Kayayyaki – CBN
An ƙaddamar da Opay a cikin shekarar 2010, da farko kamfanin ya mayar da hankali ne kan hada-hadar kuɗaɗe marasa kauri ta hanyar amfani da wayar salula. A shekarar 2020 bayan kamafanin ya samu gagarumar nasara sai ya ƙara haɓaka harkokinsa tare da dakatar da wasu ayyukansa don mayar da hankali gaba ɗaya kan hada-hadar kuɗaɗe ta hanyar amfani da wayar salula.
A cewar babban bankin Nijeriya (CBN), kashi 45 cikin 100 na al’ummar Nijeriya ne kaɗai ke mu’amala da banki, wanda hakan ke nuni da cewa, dimbin al’ummar kasar ba su da cikakken ‘yancin samun damarmakin hada-hadar kuɗi. Amma da zuwan OPay, ya dinke wannan giɓin, ya samar da yanayin hada-hadar kuɗi cikin sauƙi ta wayar salula, tare da sauƙaƙa biyan kuɗaɗen wutar lantarki da sanya katin kiran waya da saurans, duka a manhaja ɗaya.
Opay ya taka muhimmiyar rawa, ta samarwa dubban ‘yan Nijeriya guraben ayyukan yi, musamman a yankunan karkara da birane, waɗanda a baya ba sa yin amfani da bankuna, yanzun waɗannan mutane sun shigo ana damawa da su a ɓangaren hada-hadar kuɗaɗe na zamani.
Cikakken Tsarin Tafiyar Da Kudi Na Zamani Da Kamfanin Ya Ƙirƙiro Shi Ne Jigon Nasarar OPay.
Manhajar OPay ba ta tsaya kan musayar kudi kadai ba, akwai bangaren biyan kuɗaɗe, kamar biyan kuɗin wutar lantarki da sauransu. Don haka kamfanin zama mafita wajen kawar da buƙatar ‘yan Nijeriya ta zuwa kamfanoni don biyan kuɗaɗe ko kuma zuwa bankuna don tura kuɗi a koda yaushe.
A irin wannan da ake ciki a ƙasa na tsoron masu zamba ta yanar gizo, Opay ya bayar da fifiko sosai kan tsaro a manhajarsa. OPay ya gabatar da wasu mahimman hanyoyin tsaro, waɗanda suka haɗa da:
- Tsananta tsaro yayin fitar da makudan kuɗaɗe
Wannan ɓangaren yana bayar da karin kariya yayin hada-hadar manyan kuɗaɗe. Masu amfani da manhajar za su iya saita iya adadin kuɗin da zai iya fita a kullum ko a wata, ko lokaci ɗaya. Amma idan akwai buƙatar canza waɗannan ka’idoji, akwai ƙarin tsaro na musamman don tantancewa da za a buƙata don samun damar biyan buƙata nan take ta hanyar tantance fuska.
2. Tsarin samar da ƙarin tsaro cikin dare (Nightguard)
Don tabbatar da tsaron dukiyoyin al’umma a cikin dare, ɓangaren tsaro na manhajar OPay da ke aiki a dare “OPay’s Nightguard”, dole sai ya tantance fuska a yayin hada-hadar kuɗaɗe da aka yi a tsakanin 11 na dare zuwa karfe 7 na safe. Wannan yana nuni da cewa duk wata hada-hadar kuɗi ta bayan gida ko zamba ba za ta samu ba a yayin da ake barci.
3. Gano mazambata cikin gaggawa
OPay yana amfani da tsarin gano mazambata waɗanda ke sa ido kan ayyukansu, da zarar an gano alamar zamba, tsarin yana ankararwa don sake tabbatar da hada-hadar kafin ci gaba da mu’amala. Bugu da ƙari, masu amfani da manhajar za su iya kulle asusunsu ko katin cire kuɗinsu cikin sauri ta hanyar amfani da lambar USSD mai sauƙi idan wayar salular ko katin ya ɓace.
4. Tsarin Inshora na NDIC
OPay ya ƙara ƙarfafa wa masu ma’amala da shi guiwa ta hanyar daidaita matakan tsaro da Hukumar Inshorar Kuɗi ta Nijeriya (NDIC). A yanzu OPay yana bayar da ingantaccen inshora ga masu ajiya, tare da kariya har zuwa Naira miliyan 5, fiye da yadda yake a baya kan Naira N500,000.
OPay bai tsaya a tsarin hada-hadar kuɗaɗe kaɗai ba, yana bayar da tallafi don inganta rayuwar al’umma. Kamfanin yana tallafawa a fannin ilimi don ci gaban al’umma da samar da damarmaki iri-iri a faɗin Nijeriya. Kamar;
- Shirin bayar da tallafin karatu a jami’ar ABU, Zariya: A wani ɓangare na inganta rayuwar al’umma, kwanan nan OPay ya raba Naira miliyan 12 na tallafin karatu ga ɗalibai 40 marasa galihu da ke karatu a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya. Kowannensu ya samu Naira 300,000 don tallafa wa karatunsa. Wannan shiri, ya biyo bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin ABU da OPay, ya bayyana kudirin kamfanin na tallafa wa ɗalibai da kuma rage musu raɗaɗin matsin rayuwa da masu neman ilimi ke fuskanta. Wannan yunƙurin wani ɓangare ne na dabarun OPay don ƙarfafa wa matasan Nijeriya guiwa da haɓaka harkar ilimi.
- Shirin Ƙarfafa wa mata guiwa da tallafin jari don yin sana’o’i a Zariya: OPay ya kuma bayyana shirin tallafwa mata a Zariya ta hanyar samar musu da jarin fara kasuwanci da sauran sana’o’i. Wannan shirin na nufin samarwa mata sana’o’in fasaha da jari da tallafin kuɗi da ake buƙata don samun nasara a kasuwanci da bayar da gudummawa ga tattalin arziƙin cikin gida.
- Haɗin guiwar tallafin karatu tare da Jami’ar Ibadan: OPay ya kuma haɗa guiwa da Jami’ar Ibadan akan shirin tallafin karatu har tsawon shekaru 10. A kowacce shekara ɗalibai 20 da suka samu sakamako mafi kyawu, za su samu ₦300,000, wanda jimillar zai kama Naira miliyan 120 kowace shekara. Shirin zai faɗaɗa zuwa wasu ƙarin jami’o’i a fadin Nijeriya, tare da bayar da tallafin kudi ga dalibai 400 a kowace shekara, yanzu jimillar zai kama Naira biliyan 1,200,000,000 a cikin shekaru goma masu zuwa. Wannan shirin tallafin na dogon zango yana nuna irin sadaukarwar OPay da ƙarfafa guiwar ɗalibai don samar da ingantaccen Ilimi da ƙarfafa wa matasa.