ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwarzon Shekara Wajen Sauƙaƙa Mu’amalar Kuɗaɗe A 2024: OPay

by Leadership Hausa
2 years ago
Opay

OPay ya samu lambar yabo ta Jaridar Leadership ta kamfani mafi ƙwazo wajen sauƙaƙa mu’amalar kuɗaɗe ta wayar salula da yanar gizo a shekara ta 2024, saboda ƙoƙarin kamfanin na bai wa miliyoyin ‘yan Nijeriya damar faɗaɗa hanyoyin bunƙasa tattalin arziƙi, musamman ga marasa amfani da banki da waɗanda ke samun ƙalubale da bankuna a Nijeriya.

OPay ya taka rawar gani kuma ya yi fice a Nijeriya, don ya zama zakaran gwajin dafi wajen tabbatar da aminci da tsaron kuɗaɗe da sauƙaƙa mu’amala da abokan hulɗa tare da inganta tattalin arziƙin kuɗi a Nijeriya.

  • Opay, Palmpay, Kuda Da Moniepoint, Za Su Ci Gaba Da Karɓar Sabbin Kwastomomi Daga Watan Yuli
  • Babu Gudu Ba Ja Da Baya Wajen Yaki Da Hauhawar Farashin Kayayyaki – CBN

An ƙaddamar da Opay a cikin shekarar 2010, da farko kamfanin ya mayar da hankali ne kan hada-hadar kuɗaɗe marasa kauri ta hanyar amfani da wayar salula. A shekarar 2020 bayan kamafanin ya samu gagarumar nasara sai ya ƙara haɓaka harkokinsa tare da dakatar da wasu ayyukansa don mayar da hankali gaba ɗaya kan hada-hadar kuɗaɗe ta hanyar amfani da wayar salula.

ADVERTISEMENT

A cewar babban bankin Nijeriya (CBN), kashi 45 cikin 100 na al’ummar Nijeriya ne kaɗai ke mu’amala da banki, wanda hakan ke nuni da cewa, dimbin al’ummar kasar ba su da cikakken ‘yancin samun damarmakin hada-hadar kuɗi. Amma da zuwan OPay, ya dinke wannan giɓin, ya samar da yanayin hada-hadar kuɗi cikin sauƙi ta wayar salula, tare da sauƙaƙa biyan kuɗaɗen wutar lantarki da sanya katin kiran waya da saurans, duka a manhaja ɗaya.

Opay ya taka muhimmiyar rawa, ta samarwa dubban ‘yan Nijeriya guraben ayyukan yi, musamman a yankunan karkara da birane, waɗanda a baya ba sa yin amfani da bankuna, yanzun waɗannan mutane sun shigo ana damawa da su a ɓangaren hada-hadar kuɗaɗe na zamani.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Cikakken Tsarin Tafiyar Da Kudi Na Zamani Da Kamfanin Ya Ƙirƙiro Shi Ne Jigon Nasarar OPay.

Manhajar OPay ba ta tsaya kan musayar kudi kadai ba, akwai bangaren biyan kuɗaɗe, kamar biyan kuɗin wutar lantarki da sauransu. Don haka kamfanin zama mafita wajen kawar da buƙatar ‘yan Nijeriya ta zuwa kamfanoni don biyan kuɗaɗe ko kuma zuwa bankuna don tura kuɗi a koda yaushe.

A irin wannan da ake ciki a ƙasa na tsoron masu zamba ta yanar gizo, Opay ya bayar da fifiko sosai kan tsaro a manhajarsa. OPay ya gabatar da wasu mahimman hanyoyin tsaro, waɗanda suka haɗa da:

  1. Tsananta tsaro yayin fitar da makudan kuɗaɗe

Wannan ɓangaren yana bayar da karin kariya yayin hada-hadar manyan kuɗaɗe. Masu amfani da manhajar za su iya saita iya adadin kuɗin da zai iya fita a kullum ko a wata, ko lokaci ɗaya.  Amma idan akwai buƙatar canza waɗannan ka’idoji, akwai ƙarin tsaro na musamman don tantancewa da za a buƙata don samun damar biyan buƙata nan take ta hanyar tantance fuska.

2. Tsarin samar da ƙarin tsaro cikin dare (Nightguard)

Don tabbatar da tsaron dukiyoyin al’umma a cikin dare, ɓangaren tsaro na manhajar OPay da ke aiki a dare “OPay’s Nightguard”,  dole sai ya tantance fuska a yayin hada-hadar kuɗaɗe da aka yi a tsakanin 11 na dare zuwa karfe 7 na safe. Wannan yana nuni da cewa duk wata hada-hadar kuɗi ta bayan gida ko zamba ba za ta samu ba a yayin da ake barci.

3.   Gano mazambata cikin gaggawa

OPay yana amfani da tsarin gano mazambata waɗanda ke sa ido kan ayyukansu, da zarar an gano alamar zamba, tsarin yana ankararwa don sake tabbatar da hada-hadar kafin ci gaba da mu’amala. Bugu da ƙari, masu amfani da manhajar za su iya kulle asusunsu ko katin cire kuɗinsu cikin sauri ta hanyar amfani da lambar USSD mai sauƙi idan wayar salular ko katin ya ɓace.

4. Tsarin Inshora na NDIC

OPay ya ƙara ƙarfafa wa masu ma’amala da shi guiwa ta hanyar daidaita matakan tsaro da Hukumar Inshorar Kuɗi ta Nijeriya (NDIC).  A yanzu OPay yana bayar da ingantaccen inshora ga masu ajiya, tare da kariya har zuwa Naira miliyan 5, fiye da yadda yake a baya kan Naira N500,000.

OPay bai tsaya a tsarin hada-hadar kuɗaɗe kaɗai ba, yana bayar da tallafi don inganta rayuwar al’umma. Kamfanin yana tallafawa a fannin ilimi don ci gaban al’umma da samar da damarmaki iri-iri a faɗin Nijeriya. Kamar;

  • Shirin bayar da tallafin karatu a jami’ar ABU, Zariya: A wani ɓangare na inganta rayuwar al’umma, kwanan nan OPay ya raba Naira miliyan 12 na tallafin karatu ga ɗalibai 40 marasa galihu da ke karatu a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya. Kowannensu ya samu Naira 300,000 don tallafa wa karatunsa. Wannan shiri, ya biyo bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin ABU da OPay, ya bayyana kudirin kamfanin na tallafa wa ɗalibai da kuma rage musu raɗaɗin matsin rayuwa da masu neman ilimi ke fuskanta. Wannan yunƙurin wani ɓangare ne na dabarun OPay don ƙarfafa wa matasan Nijeriya guiwa da haɓaka harkar ilimi.
  • Shirin Ƙarfafa wa mata guiwa da tallafin jari don yin sana’o’i a Zariya: OPay ya kuma bayyana shirin tallafwa mata a Zariya ta hanyar samar musu da jarin fara kasuwanci da sauran sana’o’i. Wannan shirin na nufin samarwa mata sana’o’in fasaha da jari da tallafin kuɗi da ake buƙata don samun nasara a kasuwanci da bayar da gudummawa ga tattalin arziƙin cikin gida.
  • Haɗin guiwar tallafin karatu tare da Jami’ar Ibadan: OPay ya kuma haɗa guiwa da Jami’ar Ibadan akan shirin tallafin karatu har tsawon shekaru 10. A kowacce shekara ɗalibai 20 da suka samu sakamako mafi kyawu, za su samu ₦300,000, wanda jimillar zai kama Naira miliyan 120 kowace shekara. Shirin zai faɗaɗa zuwa wasu ƙarin jami’o’i a fadin Nijeriya, tare da bayar da tallafin kudi ga dalibai 400 a kowace shekara, yanzu jimillar zai kama Naira biliyan 1,200,000,000 a cikin shekaru goma masu zuwa. Wannan shirin tallafin na dogon zango yana nuna irin sadaukarwar OPay da ƙarfafa guiwar ɗalibai don samar da ingantaccen Ilimi da ƙarfafa wa matasa.
Opay
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
  • Leadership Hausa
    Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura

MASU ALAKA

Labarai

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu
Labarai

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Next Post
Sharhi Kan Dabarun Noman Dankalin Turawa

Sharhi Kan Dabarun Noman Dankalin Turawa

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.