ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

by Sulaiman
54 minutes ago
Abdulsamad

Shi mutum ne abin alfahari, kuma ɗan kasuwa wanda ya yi fice ta hanyar ci gaba da zuba jari da faɗaɗa harkokinsa duk da tsananin yanayin tattalin arzikin Nijeriya. Ta hannun BUA Group, ya ƙara zurfafa harkokin masana’antu, ya ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida, ya samar da ayyukan yi, ya gina ababen more rayuwa, ya samar da ƙima ga masu hannun jari, tare da haɓaka ayyukan agaji, abin da ya nuna amincewarsa da makomar Nijeriya. Abdulsamad Rabiu shi ne Gwarzon Shekarar 2026.

A lokacin da tattalin arziki ke cikin mawuyacin hali, a nan ne ainihin ƙimar shugabancin kasuwanci ke bayyana. Yayin da wasu kamfanoni ke samun ci gaba ne kawai lokacin da yanayi ya yi musu daɗi, wasu kuma suna nuna ƙarfinsu ne lokacin da hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru, darajar kuɗi ta ragu, kuɗaɗen samar da kayayyaki suka yi tashin gwauron zabi, kuma rashin tabbas ya mamaye al’umma. Babu shakka Abdulsamad Rabiu yana cikin rukuni na ƙarshe, ɗan kasuwa wanda muhimmancinsa bai ta’allaƙa kaɗai ga dukiyar da ya samar ba, har ma da ƙarfinsa na ginawa, faɗaɗa harkokinsa da kuma jurewa a lokacin da yanayi ke ba da dukkan dalilan ja da baya.

A lokacin da ’yan kasuwar Nijeriya ke fuskantar hauhawar farashin kayayyaki, sauye-sauyen farashin canjin kuɗi, tsadar makamashi, raguwar ƙarfin sayen masu amfani da kayayyaki da kuma ƙarin tsadar jari, Rabiu ya ci gaba da bayar da gagarumar hujja ta hanyar ayyukansa cewa: har yanzu Nijeriya ƙasa ce da ta cancanci a zuba jari a cikinta, a gina masana’antu a cikinta, kuma tana da damar samar da manyan kamfanonin masana’antu da za su iya yin gogayya a duniya.

ADVERTISEMENT

Saboda faɗaɗa masana’antun Nijeriya, samar da ayyukan yi, ƙara zurfafa samar da kayayyaki a cikin gida, zuba jari a muhimman ababen more rayuwa, samar da ƙima ga masu hannun jari, da kuma ci gaba da nuna himma wajen bunƙasa al’umma duk da tsananin ƙalubalen tattalin arziki,Abdulsamad Rabiu, shugaban BUA Group, shi ne Gwarzon Shekarar 2026.

Wannan karramawa ba ta amincewa da nasarar wasu kamfanoni kawai ba ce, har ma tana gane wata falsafar kasuwanci da ta samo asali daga wata muhimmiyar aƙida: ana samar da dukiyar da za ta dawwama ba kawai ta hanyar cin gajiyar damar da aka samu ba, har ma ta hanyar gina ƙarfin samar da kayayyaki wanda tattalin arziki ke dogaro da shi wajen bunƙasa.

LABARAI MASU NASABA

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

A shekarar 2026, an sake ganin wannan falsafa a aikaceYayin da kamfanoni da dama suka mayar da martani ga mawuyacin yanayin tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar ɗage zuba jari, rage shirye-shiryen faɗaɗa kasuwancinsu ko kuma komawa yanayin ƙoƙarin tsira, BUA ya ci gaba da ginawa.

A ƙarƙashin jagorancin Rabiu, ƙungiyar ta ƙara zuba jari a fannoni daban-daban da suka haɗa da masana’antu, samar da abinci, harkokin sufuri da dabarun raba kayayyaki, da kuma ababen more rayuwa. Ta ware ɗimbin albarkatu domin ayyukan da aka tsara ba kawai domin faɗaɗa harkokin kasuwancinta ba, har ma domin ƙarfafa tsarin samar da kayayyaki da ayyukan masana’antu da tattalin arzikin Nijeriya ke buƙata domin ci gaba.

Daga cikin manyan shirye-shiryen da BUA ya ɗauka akwai ware kusan Dala miliyan 85 domin faɗaɗa tashar BUA da ke Fatakwal. A cikin tattalin arzikin da kuɗin jigilar kayayyaki zai iya kusan yin daidai da kuɗin da aka kashe wajen samar da su, zuba jari a harkokin sufuri da rarraba kayayyaki muhimmin mataki ne wajen magance babban ƙalubalen samun damar yin gasa a kasuwa.

Faɗaɗa harkokin masana’antu bai tsaya ga tashoshin jiragen ruwa baA duk faɗin tsarin samar da abinci, BUA ya ci gaba da zuba jari a niƙan Alkama, tace sukari, samar da man girki, niƙa abincin dabbobi da kuma samar da taliya. Waɗannan fannoni suna da matuƙar muhimmanci ga rayuwar yau da kullum ta ’yan Nijeriya. Ikon samar da muhimman kayayyaki a cikin gida yana da tasiri ga wadatar abinci, samar da ayyukan yi, adana kuɗaɗen waje da kuma daidaita farashin kayayyaki.Manufar Rabiu dai ba ta sauya ba: Nijeriya ba za ta iya samun ci gaban masana’antu ta hanyar dogaro da shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje kawai ba.

Dole ƙasar ta ƙara samar da abubuwan da take amfani da su, ta sarrafa yawan amfanin gonarta a cikin gida, ta ƙara ƙarfafa hanyoyin samar da kayayyaki na cikin gida, sannan ta samar da kamfanonin da za su iya yin gogayya a babban mataki. Wannan imani ne ya kasance ginshiƙin labarin faɗaɗa harkokin BUA.

A fannin siminti, an ƙarfafa samar da sabbin masana’antu, wanda ya ƙara miliyoyin ton na siminti zuwa abin da ake samarwa a cikin gida. Ga ƙasar da ke fuskantar babban giɓin ababen more rayuwa da kuma matsalar ƙarancin gidaje da ta daɗe, samuwar kayan gini cikin sauƙi da farashi mai sauƙi abu ne mai matuƙar muhimmanci ga tattalin arziki.Ƙarin ƙarfin samarwa yana ƙara damar biyan buƙata, tallafa wa ayyukan gine-gine da kuma rage matsin lamba daga ƙarancin kayayyaki.

Kamfanin Simintin BUA ya ci gaba da ƙarfafa matsayinsa na ɗaya daga cikin manyan kamfanonin masana’antu a Kasuwar Hanyoyin Jari ta Nijeriya. Ko da a cikin mawuyacin yanayin tattalin arziki, kamfanin ya ci gaba da kasancewa mai muhimmanci ta hanyar ƙara samar da kayayyaki, inganta ayyukan gudanarwa da kuma ƙara sabon ƙarfin samarwa, tare da ci gaba da kasancewa muhimmin ginshiƙi wajen samar da ƙima mai ɗorewa ga masu hannun jari.

Wannan alaƙa tsakanin faɗaɗa masana’antu da ribar masu zuba jari na daga cikin muhimman abubuwan da za su taimaka wajen fahimtar nasarar Rabiu.

Kamfanin zamani yana da nauyin kula da buƙatun ɓangarori daban-daban. Dole ne ya gamsar da abokan ciniki, ya bai wa masu zuba jari lada, ya samar da ayyukan yi, ya tallafa wa al’ummomi, sannan ya kasance mai ƙarfin yin gasa yadda zai iya ci gaba da rayuwa. Daidaita waɗannan buƙatu na daga cikin manyan gwaje-gwajen shugabancin kamfani, kuma tsarin BUA ya yi ƙoƙarin cimma wannan buri.

Yayin da Kamfanin Samar da Abinci na BUA, wato BUA Foods ya faɗaɗa ayyukansa na samar da sukari da garin fulawa, ya ƙara ƙarfafa matsayinsa na babban mai ƙarfi a fannin kayayyakin amfanin yau da kullum a Nijeriya.

Ci gaban kamfanin ya nuna irin amincewarsa da dabarar faɗaɗa kasuwanci da kuma ƙarfinsa na shawo kan hauhawar kuɗaɗen samarwa yayin da yake gina hanyoyin samar da kayayyaki na cikin gida masu ƙarfi.Kamafanin Simintin BUA da BUA Foods sun kasance muhimman alamomin ƙarfin kamfanonin ’yan asalin Nijeriya. Girmansu da muhimmancinsu a kasuwa sun nuna cewa kamfanoni mallakar ’yan Nijeriya na iya kai wa ga matakin ƙwarewa, faɗaɗa ayyuka da kuma muhimmancin kasuwanci irin na manyan kamfanonin masana’antu masu nasara a duniya.

Sai dai lambobin kaɗai ba za su iya bayyana cikakken ma’anar aikin masana’antu na Rabiu ba.A bayan kowane sabon layin samar da kayayyaki akwai injiniyoyi, ƙwararrun masu fasaha, masu sarrafa injuna, akawu, masu rarraba kayayyaki da kuma dubban wasu waɗanda rayuwarsu ke da alaƙa kai tsaye ko a kaikaice da ayyukan masana’antu. A bayan kowace masana’anta akwai tsarin ’yan kasuwa masu samar da kayayyaki, ’yan kwangila da masu ba da hidimomi. Kowane aikin faɗaɗa masana’antu na samar da jerin damar tattalin arziki da ya zarce kamfanin da kansa.

A cikin al’ummomi a Edo, Sakkwato, Akwa Ibom da Legas, faɗaɗa ayyukan BUA ya samar da damammaki ga masu sayar da kayayyaki, ’yan kwangila da ƙwararrun ma’aikata, tare da tallafa wa ayyukan ilimi, kiwon lafiya da sauran ababen more rayuwa na zamantakewa.A nan ne ayyukan gudummawar Rabiu suka wuce fahimtar da aka saba yi game da aikin kamfani.

Kamfanoninsa ba wai kawai suna samar da siminti, fulawa da sukari ba ne. Suna kuma tsunduma cikin aiki mafi wahala da muhimmanci, wato gina cikakkun tsare-tsaren samar da kayayyaki da ayyukan tattalin arziki.Wataƙila wannan shi ne babban abin da ya bambanta harkokin kasuwancin Abdulsamad Rabiu.Ya ci gaba da gudanar da ayyukansa ne a fannoni da girman su ke buƙatar haƙuri, ɗimbin jari da kuma ɗaukar haɗari mai yawa. Masana’antu ba sana’a ce ta masu son gaggawa ba. Gina masana’antu yana ɗaukar shekaru, yayin da samar da ababen more rayuwa ke buƙatar zuba jari na dogon lokaci. Ribar zuba jari na iya samun jinkiri, kasuwanni na iya sauyawa, manufofin gwamnati na iya canzawa, darajar kuɗi na iya raguwa, sannan kuɗin makamashi na iya ƙaruwa.Duk da waɗannan rashin tabbas, Rabiu ya ci gaba da ginawa

An haifi Rabiu a Kano, inda ya mayar da abin da ya fara a matsayin sana’ar kasuwanci a shekarar 1988 zuwa ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin kamfanoni masu harkoki daban-daban a Afirka. Tafiyarsa daga kasuwanci zuwa manyan masana’antu tana kama da irin sauyin da Nijeriya kanta ke buƙata daga tattalin arzikin da ya fi dogaro da jigilar kayayyaki da amfani da su, zuwa tattalin arzikin da ke ƙara samun damar samarwa, sarrafawa da ƙara musu ƙima.

Tafiyar karatunsa ta tafi zuwa Kwalejin Tarayya ta Jihar ‘Federal Goɓernment College’, Kano, zuwa Capital Uniɓersity da ke Columbus, Ohio, inda ya karanci fannin Tattalin Arziki. Tsawon shekaru, nasarorin da ya samu sun sa jami’o’in Nijeriya da dama suka ba shi digirin girmamawa.

Amma bayan muƙamai da karramawa, akwai wani gadon tarihi mai ɗorewa: cibiyoyin masana’antu da ya taimaka wajen ginawa.Masana’antu suna wuce lokutan tashin gwauron zabi da koma-bayan kasuwanci. Ababen more rayuwa suna ci gaba da zama ginshiƙan ayyukan tattalin arziki. Ayyukan yi suna tallafa wa iyalai. Kamfanoni kuma suna samar da hanyoyin da mutane da cibiyoyi za su shiga cikin tattalin arzikin samar da kayayyaki.

Wataƙila babban gadon Rabiu shi ne ɗorewar tsarin da ya gina

Sannan akwai kuma ayyukan agaji.Ta hannun Abdul Samad Rabiu Africa Initiative, tare da ayyukan Gidauniyar BUA wato BUA Foundation, Rabiu ya faɗaɗa tasirinsa fiye da ɗakin gudanar da kamfani zuwa fannonin ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, bunƙasa matasa da kuma ƙarfafa al’umma.Ayyukansa sun ƙara mayar da hankali kan ayyukan da ke da ɗorewar amfani ga al’umma—ayyukan da ba wai kawai ake yi domin samar da taimakon wucin gadi ba, amma waɗanda ke samar da kadarori da za su ci gaba da amfanar al’umma na tsawon lokaci.

Wannan falsafa tana da muhimmanci saboda ƙalubalen da Nijeriya da Afirka ke fuskanta ba za a iya magance su ta hanyar gwamnati kaɗai ba. Dukiya mai zaman kanta, idan aka tafiyar da ita bisa alhaki da hangen nesa, za ta iya zama babban kayan aiki wajen ci gaban ƙasa.Rabiu ya rungumi wannan nauyi, ta hanyar ayyukan kamfanoni da na agaji, makarantu, cibiyoyin kiwon lafiya da sauran cibiyoyi sun amfana da tsarin bayar da tallafi da aka tsara domin samar da ƙima mai ɗorewa. A wannan fanni, yana wakiltar wata muhimmiyar fahimta da ke ƙara samun karɓuwa a shugabancin Nijeriya: cewa nasarar kasuwanci da ci gaban ƙasa ba lallai ne su kasance manufofi masu karo da juna ba.

Haƙiƙa, ’yan kasuwa masu hangen nesa sun fahimci cewa dogon lokaci na wadata da nasarar kasuwancinsu ba za su iya rabuwa da wadata da ci gaban al’ummomin da suke gudanar da harkokinsu a cikinsu ba.

Dole ne a duba tarihin Rabiu na shekarar 2026 bisa wannan babban yanayi.Bai jagoranci BUA a cikin shekara mai sauƙi ba. Yanayin tattalin arziki ya gwada masana’antun ƙera kayayyaki da masu amfani da kayayyaki baki ɗaya. Tsadar gudanar da ayyuka ta ci gaba da kasancewa, yayin da matsin lambar da ke kan kuɗin ƙasa ya ƙara wahalar shirya tsare-tsare. Hauhawar farashi ta shafi buƙata da kuma kuɗin kayan da ake amfani da su wajen samar da kayayyaki.

Sai dai martanin bai kasance na durƙushewa ba. Faɗaɗa harkoki ne. Zuba jari ne. Kuma amincewa ce da aka bayyana ba da baki ba, sai ta hanyar masana’antu, tashoshin kaya, layukan samar da kayayyaki da kuma tsare-tsaren dogon lokaci.Wannan amincewa tana da muhimmanci fiye da BUA kaɗai. Lokacin da ɗaya daga cikin manyan ’yan masana’antun Nijeriya ke ci gaba da zuba jari mai yawa a ƙasar, yana aikawa masu zuba jari, ma’aikata, masu samar da kayayyaki da matasa ’yan kasuwa saƙon cewa ƙalubale ba lallai ne ya zama dalilin miƙa wuya ba. Mawuyacin yanayi na iya haifar da ƙirƙire-ƙirƙire. Matsin tattalin arziki na iya tilasta inganta yadda ake gudanar da ayyuka. Rashin tabbas kuma na iya zama dama ga waɗanda suka shirya kallon abubuwa na dogon lokaci.

Wannan shi ne ƙarfin hali na harkokin Abdulsamad Rabiu, ƙarfin hali da aka haɗa da iya aiwatar da buri.

Tsawon shekaru, Nijeriya ta yi ta magana game da masana’antun cikin gida a matsayin buri. Rabiu ya taimaka wajen mayar da wannan buri zuwa zahiri: murhunan siminti da injinan niƙa, matatun mai da masana’antu, ɗakunan ajiya da kayayyakin sufuri da rarraba kayayyaki, cibiyoyi da aka haɗa ta hanyar damar samar da kayayyaki da harkokin kasuwanci ke bayarwa.

Saboda haka, nasarar da ya samu ba wai kawai ya gina babbar ƙungiyar kamfanoni mai nasara ba ce, abin da ya fi muhimmanci shi ne cewa ya ci gaba da ginawa ko da lokacin da yanayi ya yi wuya.Saboda jagorancinsa mai hangen nesa; domin faɗaɗa ƙarfin masana’antun Nijeriya a lokacin rashin tabbas na tattalin arziki; saboda samar da ayyukan yi da damammaki a sassa daban-daban na tsarin samar da kayayyaki; saboda ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida da rage dogaro da shigo da su daga ƙasashen waje; saboda zuba jari a muhimman ababen more rayuwa; saboda samarwa da kuma ci gaba da ƙarfafa ƙimar hannun jari; saboda nuna dogon lokaci na amincewa da tattalin arzikin Nijeriya; da kuma saboda yaɗa amfanin harkokin kasuwanci ta hanyar ayyukan agaji da zuba jari mai tasiri ga al’umma,Abdulsamad Rabiu, Shugaban BUA Group, Shi Ne Gwarzon Shekara Na 2026A wajen karrama shi, LEADERSHIP ba wai ta karrama shi a matsayin ɗan kasuwa mai gagarumar nasara kawai ba ce, har ma tana karrama wani mai masana’antu wanda saƙonsa mafi ƙarfi ya bayyana ne ta hanyar siminti, ƙarfe, masana’antu da damammaki.

Abdulsamad
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya
  • Sulaiman
    Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
  • Sulaiman
    Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya
  • Sulaiman
    Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

MASU ALAKA

Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe
Manyan Labarai

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje
Labarai

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO
Labarai

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026

LABARAI MASU NASABA

Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026
Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

Sin Ce Ta Zo Ta Farko A Rahoton Yanayin Tsaron Jama’a Na Duniya

September 10, 2026
Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Ciri Tuta Game Da Rawar Gani Da Take Takawa A Fannin Warware Kalubalen Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.