Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Peter Obi, ya ce ba zai janye wa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba.
Obi ya bayyana cewa batun haɗa kai tsakanin ’yan adawa da kuma wanda zai tsaya takarar shugaban ƙasa a madadin ƙawancen ba zai kasance shawarar mutum ɗaya ba, sai dai abin da za a cimma ta hanyar tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki.
Ya kuma bayyana cewa NIjeriya na bukatar sauyin shugabanci, yana mai jaddada muhimmancin samar da tsarin siyasa da zai ba ’yan ƙasa damar zaɓar shugabancin da suke ganin zai iya magance matsalolin ƙasar.
A cewar rahoton, kalaman Obi na zuwa ne yayin da ake ƙara samun tattaunawa tsakanin manyan ’yan adawa gabanin zaɓen 2027, musamman kan yiwuwar kafa ƙawancen da zai fafata da jam’iyyar APC.
Sai dai Obi ya nuna cewa duk wani shiri na haɗin gwiwar ’yan adawa dole ne ya kasance bisa tsarin da aka amince da shi tare da tattaunawa, ba wai mutum ɗaya ya yanke shawarar wanda zai janye ko wanda zai tsaya ba. Saboda haka yanzu shi a matsayinsa na Peter ba zai iya janye wa ba, sai dai a matakin jam’iyya ta amince ko karta amince.













